Connect with us

LABARAI

An Cafke Mutum 5 Bisa Zargin Kitsa Sabon Rikicin Makiyaya Da Manoma A Jigawa

Published

on

Rundunar ‘yansanda reshen jihar Jigawa ta ce tayi nasarar cafke mutane biyar bisa zargin kisan wani Manomi mai suna Alhaji Sama’ila Mai unguwar Yabaza sakamakon barkewar rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma a yankin.

Kakakin rundunar ta ‘yansanda reshen jihar, SP Abdul Jinjiri ne ya bayyana wannan alwashi yayin zantawarsu da wakilinmu a birnin Dutse.

Ya ce manomin dan shekara 80 da haihuwa mai suna Alhaji Sama’ila mai unguwa ya rasu bayan da rikicin ya barke tsakanin fulani da manomaa daren ranar litinin a kauyen Iggi dake karamar hukumar birnin Kudu a jihar ta Jigawa.

Haka kuma ya karada cewa, har yanzu rundunar tasu ta baza jami’anta domin cigaba da zakulo duk masu hannu cikin sanadiyyar tashin wannan rikici a yankin.

A cewarsa yayin zantawarsa da majiyarmu a birnin Dutse, shugaban kungiyar Makiyaya (Miyetti Allah cattle breeders) Malam Sa’idu Musa Gagarawa ya ce rikicin ya farane bayan da wasu manoma suka farwa wasu fulani su biyu, yadda daka bisani suma suka gayyato ‘yan uwansu suka afka wa manoman kuma suka halaka mutum daya tare da raunata wasu da dama.

“Akasin da aka samu shi ne kafin a sanar da hukuma tuni wadannan fulani sunyi gungu kuma sun je sun dau fansa wadda yayi sanadiyyar halaka mutum daya da raunta wasu,” ‎in ji shugaban.

Haka kuma ya tabbatarda cewa, rikicin ya fara ne sanadiyyar filin kiwo a jejin Yabaza da ke kauyen na Iggi wadda kowannensu keson ya zama karkashin ikonsa.

”Wannan rikici da ya faru kan wannan jeji wadda tun shekaru a baya shugabanni suka mallakawa Fulani amma wasu marasa son zaman lafiya suke tada fitina,” I nji shugaban Miyetti Allah.

Tuni dai hankali ya kwanta a yankin da abin ya faru.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!