Connect with us

Da dimi-diminsa

Boko Haram Sun Kai Wa Gwamnan Borno Hari

Published

on

A daren jiya ne ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai wa tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum farmaki.

Farmakin ya afku ne da misalin karfe 9:00 na dare.

Kamar yadda majiyarmu ta TheCable ta ruwaito, majiya mai tushe daga bangaren jami’an tsaro ta tabbatar da cewa ‘yan ta’addan na Boko Haram sun kai wa tawagar gwamnan Hari ne a Konduga, yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta komawa Maiduguri daga Karamar Hukumar Bama.

Gwamna Zulum ya ziyarci Kananan Hukumomin Bayo, Kwaya, Kusar, Askira Uba da Gwoza a wani zagaye da tawagarsa ke yi domin duba mutane da wuraren da ke bukatar tallafi.

Majiyar tamu ta tabbatar da cewa, gwamnan da kwamishinoninsa dai sun tsallake rijiya da baya ba tare da wani abu ya same su ba, sai dai mota ta karshe a tawagar, wata motar sojoji ce kawai a ka samu da harsasai.

“A daidai lokacin da suka bude mana wuta, sai su ma jami’an tsaro suka mayar musu da martani, wanda hakan ya rusa shirin kwantar baunarsu.

Ita dai Konduga tana kusa ne da gawurtaccen dajin nan na Sambisa, inda sansanin ‘yan boko haram reshen Abubakar Shekau suke da mafaka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: