Connect with us

TATTAUNAWA

Gwamnatin Filato Za Ta Rushe Duk Wani Gini Mai Hadari Ga Rayuwar Mutane – Kefas John

Published

on

Mista Kefas John, shi ne mukaddashin shugaban Hukumar Raya Birane da Tsabtace Muhalli ta Jihar Filato, (JMDB). Wakilinmu da ke Jos, Lawal Umar Tilde, ya samu damar tattaunawa da shi a kan hadurran faduwar gidaje da  aka samu a garin Jos wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa kwanakin da suka gabata, ga yadda hirar tasu ta kasance:

Gwamna Simon Bako Lalong, ya bada umurni a rusa duk wani gini da aka samu yana da hadari ga mutane su zauna a cikinsa, kasancewar wannan ma’aikata da kake jagoranta ita ce take lura da tsarin gine-gine a wannan jiha, ya zuwa yanzu wane mataki ka dauka?

To na gode da wannan tambayan, daman can muna kiyayewa bisa abubuwa irin wadannan domin ba za mu so ba mutane surika gine-gine barkatai ba bisa ka’idaba wadansu ma za ka samu akan hanyan ruwa suke gina gedajensu saboda haka tun kafin gwamna ya bada wannan umurni mun bada notis wa masu irin wadannan gine-gine da basu da tsari mai kyau a cikin wannan garin Jos da kewaye  ba tare da sun zo nan sun nemi izni daga wajemmuba. Akwai gidaje da dama da muka ba da notis wa masu su domin mun lura sun aza harsashin gininsu ba tare da sun nemi shawaran kwararru ba.

Ko zan iya sanin yawan gidajen da kuka basu notis da wadanada kuka rusa ya zuwa yanzu da nake magana da kai?

Mun bada notis wa mutanen da yawa domin ma’aikatammu kullum sukan zaga cikin gari da kewaye suna duba irin gine-ginen da ake yi kuma mun fara rushe gidajen mutanen da muka basu wa’adi ya cika basu  dau matakin yin gyra ba domin ba za mu bari irin abubuwan da suka faru a kwanakin baya inda aka sami asarar rayuka mutane sama da ashirin a sanadiyar faduwar gidaje a cikin wannan garin.

To mene ne shawararka ga irin wadannan mutane da suke irin wadannan gine-gine ba tare da sun nemi shawarar kwararruba ko su zo nan ofis su nemi izninku kafin su fara gini?

Shawarar da zan byar a nan ita ce duk mutumin da yake da fili zai yi gini, ya zo nan ofis ya nemi izni wajen wannan hukumar domin ita hukumar an yi ta ne don taimakawa mutane ba musguna masu ba, ita huka ma idan aka sanar da ita za ta je ta ga wurin ta ba da shawara yadda za a sami yin gini ingantacce don haka muke bukatan dukan mutanen da suke da filaye cikin garin da kewaye idan suka tashi yin gini su rika tuntubammu su bamu cikakken hadin kai don kauce wa ire iren haduran da suka auku a kwanakin da suka gabataba.

Kasancewar wannan bashi ne karon farko ba a garin nan da ake samun asarar rayuka a hadarin faduwar gidajen musamman a lokacin damina irin wannan, wane irin tsari ne wannan hukuma za ta bullo da shi wajen hana aukuwar irin wadannan hadura a ciki da wajen garin Jos nan gaba?

Don tabbatar da an sami nasarar tsaida faruwan irin wannan nan gaba wannan hukuma na aiki kafa da da kafada da ma’aiktar kasa da Safiyo na jiha wajen kididdiga yawan gidajen da ake ginawa a bisa ka’ida ba, musamman masu yin gini a kan hanyar ruwa do cikin rafi, to kaga irin wadannan gidajen duk za su koka, kuma shi ya muke kokarin hana yin gini a irin wadannan wurarin.

Mai girma Gwamna Simon Lalong ya cika kwana dari a wa’adin mulkinsa na biyu, kasancewar kana aiki tare da gwamnan me ye za ka ce wa mutane game da manufofinsa?

Abin da zance a nan shi ne mutane su yanka wa kawunansu hukunci a kan yadda ya sami jihar da kuma yanzu bayan ya yi shekara hudu a ofis, kowa ya sani a jihar nan an sami kyakywan canji a kowane gaggari
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!