Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ja-in-ja Ta Karu Tsakanin Sha’aban Da Ishak Kan APC A Birnin Kano

Published

on

Da alama dai rashin jituwa na dada ruruwa a tsakanin ‘yayan jam’iyyar APC a karamar hukumar Birnin Kano tsakanin tsagin dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, da a ke yi ma sa ganin a yanzu shi ne ya fi cancanta ya zama jagoran APC a yankin a matsayinsa na zababben dan majalisa da bangaren tsohon shugaban karamar hukumar kuma tsohon kwamishina a jihar na majalisar zartarwar da ta gabata, wanda har yanzu ba a sake nada ta ba tun bayan lashe zaben kujerar gwamna a karo na biyu da gwamnatin APC a jihar ta Kano, wato Hon. Muktar Ishak Yakasai.

A na ganin cewa, babban abinda ya haifar da wannan takaddama shi ne, akwai tsarin jagorancin jam’iyyar da a ke da shi tun kafin Hon. Sharada ya sami nasarar zama dan majalisar tarayya da a ke jagorantar APC a yankin birnin da shi karkashin jagorancin Hon. Yakasai, a matsayinsa na tsohon shugaban karamar hukuma kuma tsohon kwamishina, wanda ya yi neman takarar kujerar majalisar tarayya tare da Sha’aban din a zaben da ya gabata.

Jagorancin na Muktar Ishak ya na da goyon bayan tsohon dan majalisar dokokin jiha na Birni da kewaye, wanda shi ne shugaban hukumar KAROTA a yanzu, wato Baffa Babba Dan’Agundi da kuma goyon bayan shugaban karamar hukumar birnin Kano mai ci yanzu, Alhaji Sabo Dantata da sauran jiga-jigan jam’iyyar na Birni da kewaye.

Duk wani kulle-kullen siyasa na APC a cikin yankin Birni a na yin sa a tsakanin mutane uku da a ka zayyano a baya su ke kullawa, su warware.

Zuwan Sha’aban Ibrahim Sharada cikin harkar siyasar Birnin Kano tun fari na da dangantaka ne da mukami da Shugaba Buhari ya ba shi na mai taimaki ma sa na musamman a kan radiyo da talabishin, wanda ya yi amfani da wannan dama ta jan ’yan jam’iyya a jiki da kuma gudanar da ayyuka na tallafa wa al’umma a bangarori daban-daban.

A na danganta hakan da kuma irin tasiri da karbuwa da ya soma samu, wacce ta sa jagorori da ke juya siyasar APC soma ganinsa a matsayin barazana a gare su. Don haka nema a ka shiga saka ma sa waigi tsakaninsa da ’yan jam’iyyar tun daga matakin akwatuna da mazabu, kamar yadda wani jigo a jam’iyyar ya shaida wa wakilinmu a Kano.

Ya ce, sau da dama idan Sha’aban ya shirya wani taro ko ya raba wani ihsani ga ’yan jam’iyyar ba a bari su je, ko su karba idan ya aiko mu su, inda an sha ladabtar da wadanda su ka bijire ta hanyar cire su daga wani mukami da su ke a kai.

Rashin jituwar ta dada kamari ne a lokacin da Sha’aban ya nuna muradinsa na neman tsaya wa takarar dan majalisar tarayya a daidai lokacin da jagoran APC na karamar hukumar, Alhaji Muktari Ishak Yakasai, shi ma ya ke takarar neman kujerar.

Ko a lokacin da a ka gudanar da zaben fidda gwani na ’yan majalisun tarayya na ’yar tinke, an sami ja-in-ja da kowanne ke ikirarin nasara, inda da ta kai ga tafiya kotuna har a ka kai ga hukuncin karshe na tabbatar da Sha’aban a matsayin wanda ya yi nasarar zama dan majalisar tarayya na a Birni sakamakon nasarar lashe babban zabe da APC ta yi na dan majalisar tarayya na birnin Kano kuma babbar kotun koli ta tabbatar da nasara ga Sha’aban.

Sai dai a na ganin samun damar wakilcin Birni da Sha’aban ya ke a ke ganin ya soma daukar hanya na kokarin yin ramuwar gayya ga wadanda ke yi mu su biyayya a matsayin jagorori da dattawan APC a karamar hukumar Birni.

Hakan ya fito karara ne kuwa sakamakon wani taro da ya kira da wani bangare na dattawan APC da ya sanar da cewa an rushe shugabancin dattawan APC na birnin, wanda Ambasada Kabiru Rabiu Dansitta ke shugabanta, a ka maye shi da na riko karkashin jagorancin Abubakar Muhammadu Kingibe, wanda shi ne ya yi daraktan yakin neman zaben Sha’aban din a lokacin zaben da ya gabata.

Wannan ya sa shakku a zukatan wasu ’yan jam’iyyar har su ke yiwa abin kallon wata dama ce ta ramuwar gayya da dan majalisar tarayyar ke shirin yi.

Sai dai wata majiya ta bayyana ma na cewa, tsarin nasu Sha”aban ba shi da wani tasiri kuma ba zai yiwu ba, domin ba shi ne zai fitar da jagorori ba, saboda jagoranci yarda ce ta al’umma, ba mutum daya ba, don ya na da dama.

Sai dai wasu na zargi da danganta cewa irin daurin gindi da dan majalisar ya samu a wajen Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma shugaban jam’iyyar na jiha na da dangantaka da shirin karbe jagorancin APC da ya ke a Birnin Kano.

Wasu kuma na ganin matakin a ce an rusa shugabancin shi zai bada dama a kwace karfin fada a ji da wanda a ke gani a matsayin jagoran jam’iyyar, Alhaji Muktari Ishak Yakasai, da na kusa da shi, wato Baffa Babba Dan’Agundi, su ke da shi da ta haka ne kawai za a iya kange su daga fada a ji.

Sai dai kuma a kokarin wakilinmu na jin daga dukkan bangarorin mun buga wa Muktar Ishak Yakasai waya, amma ba ta shiga ba, mun kuma aike ma sa da sakon kar-ta-kwana bai ce komai a kai ba.

Shi ma mun nemi jin ta bakin Hon. Sha’aban Ibrahim, dan majalisar tarayya na birnin Kano, ta hanyar tura ma sa sakon kar-ta-kwana, amma bai amsa ba har lokacin kammala hada wannan rahoton.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!