Connect with us

MANYAN LABARAI

Kamun Ludayin Sabbin Gwamnonin Arewa A Cikin Kwana 100 Na Mulki

Al’ummomin jihohin da suka samu sababbin gwamnoni a zaben 2019, sun fara dora gwamnonin a kan sikeli, da yake sun cika kwana dar har da doriya a kan mulki. Domin ganin irin kamun ludayin sababbin gwamnonin, wakilanmu da ke wadannan jihohin sun tattaro bayanan abubuwan da suka shuka a cikin kwana darin da suka a kan karagar mulki. Ga rahotannin nasu kamar haka:

Kokarin Da Gwamnan Bauci Ya Yi A Kwana 100 Na Mulki

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A Larabar 29 ga watan Mayu, 2019 ne da misalin karfe 11:35 na safiya, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, na jam’iyyar PDP ya amshi rantsuwar kama aiki da alkawarin gudanar da kyawawan ayyukan raya jihar Bauci a matsayin zababben gwamna mai cikakken iko a jihar.

A yau Juma’a, 6 ga watan Satumba, ne gwamnnan yake cika kwanaki 100 cik a bisa karagar mulkin jihar, don haka, za mu yi waiwaye kan kamun ludayin gwamnatinsa da kuma alkiblar da ta sanya a gaba.

LEADERSHIP A Yau Juma’a ta shaido cewar Sanata Bala dai shi ne gwamna na shida a cikin jerin zababbun gwamnoni da jihar ta Bauci ta yi, inda ya kayar da gwamna mai ci Muhammad A. Abubakar, na jam’iyyar APC da kuri’u masu dama.

Bala, ya samu nasarar zama gwamnan Bauci ne da kuri’u 515,113; a yayin da tsohon gwamnan jihar, Muhammad A. Abubakar (APC) ya samu kuri’u 500,625 a matsayin wanda ya zo na biyu; PRP ta samu 46,326; a yayin da kuma GPN ta samu kuri’u 2,304 kacal.

Babbar Jojin jihar Bauci, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar, ce ta rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Bauci. inda shi kuma ya rantse da Alkur’ani mai Girma wajen daukar alkawarin gudanar da kyawawan ayyuka domin ciyar da jihar Bauci gaba.

A cikin jawabin da ya yi wa al’ummar jihar Bauci na kama aiki, gwamnan jihar Bauci, Sanata Bala Muhammad ya shaida cewar ya zo kan wannan kujerar ne domin ya bayar da tasa gudunmawar wajen kyautata jihar Bauci da kuma yi mata zubi na kwarai.

Ya ce, zai bayar da fifiko wa sashen harkar noma, lafiya, ilimi da kuma tabbatar da bunkasa kudaden shiga domin samar wa jihar hanyoyin samun kudaden shiga domin tabbatar da kai jihar matakin da ya kamata.

Ko a lokutan da yake yawon neman a zabe shi, gwamna Bala ya shaida cewar gwamnatinsa za ta tabbatar da kyautata birane da karkara, samar wa matasa ayyukan yi, rage kaifin talauci da kuma kyautata harkar noma, ilimi, lafiya da sauransu.

A yau da gwamnan ke cika kwana 100 za mu duba mu ga wacce rawa ya taka ko ya fara takawa domin tabbatar da cika wa al’ummar jihar alkawuran da ya yi masu.

Ba shakka, gwamna Bala ya himmatu wajen bayar da kwangilolin shinfida sabbin tituna da kuma yi ma wasu kwaskwarima a ciki da wajen jihar; wanda hakan muddin aka kai ga kammala wadannan ayyukan za su kawo ci gaba ta fuskacin kyautata rayuwar al’umma.

Aikin farko na shimfida tituna da ya fara bayarwa su ne; A ranar 22 ga watan Yuli, ya kaddamar da aikin shimfida tituna guda biyu da kuma kwaskwarima wa tituna guda biyu a cikin kwaryar jihar domin bunkasawa da kyautata rayuwar jama’ar jihar.

Ayyukan wadanda gwamnan ya kaddamar za su lakume sama da naira biliyan biyar masu nisan kilomita 10.4 da ake sa ran kammala ayyukan nan da wata shida. Ayyukan sun hada da shimfida sabon titi fil-a-ledarsa da ya tashi daga Layin Ibrahim Bako ya zarce har babban titin Maiduguri Bye-Pass, da kuma shimfida sabon titi wanda ya tashi daga layin Sabon Kaura ya nausa har zuwa kan hanyar Jos.

Tituna guda biyu da aka bayar da aikin yi masu kwaskwarimar kuwa sun hada da titin kasuwar Muda Lawan da kuma titin Yakubun Bauci.

A ranar 31 ga watan Yuli, gwamnan ya kaddamar da aikin shimfida sabon titin da ya tashi daga Sade Zuwa Akuyam, wannan aikin zai lashe naira biliyan 3 rus. Aikin mai nisan kilomita 16.2, titin dai ya hade kananan hukumomi biyu na Darazo da Misau.

Har-ila-yau, a ranar 24 ga watan Agustan 2019, Gwamna Bala ya kaddamar da fara aikin titi mai nisan kilomita 58 wanda zai hade kananan hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa. Aiki ne wanda zai ratsa yankunan Yalwan Duguri, Badaran Dutse, Birim, Bajama, Kumbala, Kundak, Wurno da kuma yankin Burga da ke karamar hukumar Tafawa Balewa da Kuma Alkaleri. An bayar da wannan aikin ne a kan kudi naira biliyan takwas (8).

Sauran ayyukan raya birane da karkara da Gwamnan ya bayar sun hada da aikin da ya tashi daga GRA Azare zuwa old Kano a karamar hukumar Katagum.

Baya ga fannin shinfida tituna, a cikin nasarorin da gwamna Bala ya samu na zama gwamnan jihar Bauci, ya iya cimma nasarorin janyo wa jihar Bauci kungiyoyi da hukumomi daban-daban su kawo ababen ci gaba kama daga fuskar ilimi, lafiya da sauransu.

Gwamna Bala Muhammad Abubakar, ya iya nada kwamishinonin 20 a cikin kwana 100, kana ya nada shugabanin riko na kananan hukumomi 20 gami da wasu manyan nade-nade da ya gudanar a cikin kwana 100.

A cikin nasarorin gwamna Bala ya iya rabar ma wasu asibitoci motocin dauko marasa lafiya domin kyautata kiwon lafiya, sannan ya kuma rabar da wasu kayyakin tallafi na amsar haihuwa da daman gaske hadi da na’urorin aiki ga jami’an da suke amsar haihuwa, sannan gwamnan ya dauki nauyin gudanar da aikin jinya kyauta na tsawon kwanaki uku.

Daga cikin hubbasawar gwamna Bala na samar wa jihar tallafi daga sassa daban-daban, babban bankin duniya ta bayar da tallafin kudade domin kyautata koyo da koyarwa a jihar. Makarantu guda dubu daya da dari uku da ashirin 1,320 da suke fadin kananan hukumomi biyar na jihar Bauci ne suka samu nasarar cin gajiyar shirin kyautata makarantu na Bankin duniya ta shekarar 2019.

A bangaren kyautata ruwan sha, a kwanakin baya gwamnan jihar ya kaddamar da aikin gyara dam-dam da hanyoyin raba ruwan amfanin yau da kullum a jihar, wannan aikin da ke gudanuwa hadin gwiwa ne da masu bayar da tallafi.

A bangaren ilimi kuwa, jihar Bauci ta samu tallafin biliyan biyu daga hukumar kula da ilimi a matakin farko ta tarayya UBEC domin inganta koyo da koyarwa a jihar Bauci. Sannan, gwamnan ya sanya hannu da kasar Faransa domin kyautata tattalin arzikin jihar. Da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa da na tarayya da suke baiwa jihar ta Bauci tallafi domin ci gaba duk a bisa kokarin gwamna mai ci. Ko a jiya ma, jihar ta samu tallafin Babura sama da guda 115, da kuma littafai sama da miliyan guda duk domin kyautata harkar ilimi a jihar wadanda ta samu daga UBEC.

Wani abin burgewa da gwamna Bala, yana sanar da fara jan ragamar shugabacin jihar da sanar da duniya hakikanin ababen da jihar take samun tallafinsu, don kuwa gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin naira miliyan 800 domin gyara barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar, gwamnan ya shaida da bakinsa cewar wannan tallafin daga gwamnatin tarayya ya zo, fadin inda aka samu tallafin ya taimaka ganin jihar ba ta saba samun bayani irin wannan ba, inda a wasu lokutan ba a bambance aikin gwamnatin tarayya da na jihar.

Daga cikin alkawuran da gwamnan Bauci ya yi wa jama’an jihar har da kokari domin kyautata rayuwar matasa da shawo kan zaman kashe wando, sai dai har zuwa yanzu matasan ba su fara ganin wani shiri na musamman da aka yi don su ba, sai dai suna fatan gwamnan zai dube su.

Dangane da batunsa na biyan kudin giratuti da fansho kuwa, Gwamnan jihar Bauci, ya biya naira miliyan dari 100 domin fara biyan kudaden Giratuti da tsoffin ma’aikatan jihar ke bin gwamnatin bashi, ana sa ran zai ci gaba da biyan wannan kudin lokaci-bayan lokaci.

Kamun ludayin gwamnan a kwanaki 100 tamkar za a iya cewa zai tabuka abun a zo a gani musamman da yake ma’aikata har zuwa yanzu ba su fara korafi ba.

Rawar Da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazak Ya Taka A kwana 100

Daga Khalid Idris Doya

Tun ranar da aka rantsar da AbdulRahman AbdulRazak, a matsayin zababben gwamnan jihar Kwara a ranar 29 ga watan Mayun 2019, wanda a yau yake cika kwana 100 a karagar mulki ya samu nasarar gudanar da wasu ayyukan raya jihar.

Gwamna AbdulRahman, dai shi ne zababben gwamna na bakwai a cikin jerin gwamnan jihar a karkashin mulkin demokuradiyya da jihar ta yi.

A lokacin da aka rantsar da gwamnan ya sha alwashin cewar arzikin jihar ba zai ke tafiya a watse ba, za su yi kokari wajen tabbatar da ririta dukiyar jihar da tafiyar da ita ta hanyoyin da suka dace. Domin kokarinsa na rage kashe dukiyar jihar watanni uku ya shafe yana amfani da motarsa ta kashin kai.

AbdulRazak ya fara kama mulki da tara masu ruwa da tsaki a jihar da kuma manyan jami’an gwamnati wajen shaida masu shirinsa na kai jihar mataki na gaba da kuma rangadi domin gane wa idonsa yanayin da ake ciki musamman makarantu.

A bisa riskar jihar da sabon gwamnan ya yi da tulin matsaloli ga kuma tulin bashi na naira biliyan N80 da ake bin jihar, hakan ya sanya ma kafar sadarwa ta rediyo mallakin jihar ta daina aiki, sannan jihar tana kuma cike da wasu matsaloli masu yawa a lokacin da ya amshi mulkin jihar.

A cikin kokarin sabon gwamnan a kasa da kwana 100 gidan rediyo mallakin jihar ta Kwara ya dawo aiki, gidan talabijin na jihar Kwara shi ma ya dawo aiki.

Sannan gwamnan ya kuma tabbatar da shawo kan matsalolin ruwa da suke addabar wasu yankunan Ilorin, ciki kuwa har da babban asibitin jihar.

Ya yi kwaskwarima da gyara ma’aikatun ruwa a Illorin, Lafiagi, Patigi da kuma Igbaja wanda yanzu haka kaso 95 cikin dari tuni aka kammalasu. Gwamnan ya gyara famfunan burtsatse guda 400 a fadin jihar domin shawo kan matsalolin ruwa da jihar ke fuskanta.

Kwalejin ilimi, gwamnan ya tashi tsaye wajen tabbatar da ta dawo bakin aiki, inda ya biya albashin da suke bin tsohowar gwamnati bashi, sannan an kuma tabbatar da samar da sahalewa da amince wa ga wasu kwasa-kwasai da dama a cikin kwalejin.

A bisa kokarin biyan bashin naira miliyan 450, ckin sauri UBEC ta sa farfado da jihar Kwara daga halin da take ciki. Makarantar koyar da ilimin aikin Anguzoma, yanzu haka sun samu amincewa da tantance wa.

A kwana-kwanan nan, gwamnan ya bayar da kaso na hadaka na naira miliyan 232 domin shawo kan yawaitar mace-macen yara kananan, matsalar karancin abinci mai gina jiki, cutar kwalera da sauran matsalolin lafiya. Wannan matakin ya kai jihar Kwara da samun dama kan asusun tallafin lafiya domin taimaka wa marayu da marasa galihu da sauran jama’a.

A bangaren gyara birane da samar da tituna, gwamnan ya gyara tituna da dama domin taimaka wa jama’a wajen sawwake musu zirga-zirga. Gyaran gadoji na Oke Foma.

Gwamnan Kwara ya kaddamar da aikin hanyoyi guda 13 da za a shimfidasu a fadin shiyyoyin sanata uku da suke jihar.

Gwamnan ya biya kason hadaka na farko na miliyan 200 wanda yanzu haka jihar Kwara ta samu damar cin gajiyar dala milyan 60 domin shawo kan matsalolin ruwa, albarkatun gona na babban bankin duniya.

Yanzun haka ‘yan kwangilar aikin hanya na Gwanara da ke Baruten sun dawo sun ci gaba da aiki. yanzun haka aikin hanyar CocaCola a Illorin na ci gaba da gudanuwa.

Yanzu haka kotuna guda biyu na Center Igboro da Sango gwamnatin ta masu kwaskwarima da gyara su. Kuma yanzu haka ana kokarin gyara dakunan wasu kotunan.

A cikin nasarorin gwamnan Kwara a kwana 100, a yunkurinsa na kare rayuwa da dukiyar jama’a, gwamnan ya gyara hadi da yin kwaskwarima wa gidan yarin Illorin.

Yanzu haka gwamnan ya yi aiki sosai wajen kammala aikin sabuwar sakatariyar jihar wanda kwanan nan za a kaddamar kamar yadda gwamnatin ke cewa. A watan Yuni gwamnan ya baiwa ‘yan kwangilar da ke aikin naira miliyan 350 don su ci gaba da aikin.

A bangaren kyautata ma’aikata kuwa, a kowane wata gwamnan na kokarin biyan kudaden gudanarwa domin aiki yake tafiya yadda aka tsara.

Jihar Kwara za ta samu cin gajiya daga cikin naira biliyan 200 na babban bankin duniya don samar da hannun jari da masana’antu da kuma samar da kamfanonin da aka tsara domin cin gajiyar mata da matasa.

Tsaron Da Gwamna Matawalle Ya Samar A Zamfara Ya Bude Sabon Babin Ci Gaba

Daga Hussaini Baba,Gusau

Da yake masu iya magana na cewa ‘waiwaye adon tafiya’, jimkadan  bayan  bayyana sakamakon  zaben da ya gabata na Gwamnoni da ‘yan majalisun na tarayya da na jahohi cewa Jam’iyar APC ce ta lashe zaben gaba daya a fadin jihar Zamfara , Dan takarar Gwamnan na Jam’iyyar PDP, Hon Bello Muhammad Matawalen Maradun ya bayyana cewa ‘Su ne za’a rantsar a matsayin wadanda suka lashe zaben dan jam’iyyyar APC, ba su da ‘yan takara, dan ba su yi zaben fid da gwani ba.

Haka kuwa abun ya kance  ‘Yan takarar APC da Hukumar Zabe ta bayyana a matsayin wadanda za’a rantsar a ranar 29 ga watan mayu, kowa na ta shirin shiga ofis, sai ga hukuncin daga Babbar Kotun Kasa ta bayyana cewa ‘ Jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara, dan haka hukumar zaben mai zaman kanta  ta gaggauta bawa jam’iyyar da ta zo ta biyu nasara a zaben a Zamfara.

Wannan ne ya sa Jam’iyyar PDP ta tsinci dami ga kala, ta zamo ita ce mai kujerin ‘Yan majalisar Dattawa da na Wakilai da kuma kujerar Gwnamnan Jihar da ‘Yan majalisun jihar baki daya .

Kwana biyar da Kotu ta ba Jam’iyyar PDP jihar Zamfara aka rantsar da su a ranar 29 /5/ 2019 .

A wajan rantsar da Gwamna Bello Muhammad Matawalen Maradun ya dau alwashin kawo zaman lafiya da kuma amso wadanda a kai garkuwa da su daga hannun mahara da ke cikin dazuka .

Aikin farkon da Gwamna Bello Matawalen Maradun ya fara yi shi ne na ziyara gidan Marayu inda a nan ta ke da ya ji Matsalolin da Gidan yake ciki da su Marayun ya tausaya masu idonsa cike da kwalla ya kuma tabbatar masu da cewa ya basu rabin albashinsa na kowane wata har ya kamala mulkinsa, kuma yanzu haka watana uku kenan da fara amfana da wannan.

Matsalar tsaro kuwa, Gwamna Bello Muhammad Matawalen ya fara samun bakin zaren ne daya Haramta kungiyar ‘Yan sakai ,kuma ya umarci Fulani da suke ta’addanci da su aje makamansu su zo a sasanta, dan shima Bahillace ne ba zai yiwu ba a ce Fulani basu da gata a jihar da dansu ke mulki ba.

Taka wa ‘Yan sakai birki da Gwamna Matawalen Maradun ya yi ne ya fara samun nasarar magance matsalar tsaron da ta’addabi jihar, dan a lokacin gwamnatin da ta gabata bahilace baida ikon Sakamakon sulhu da Gwamna Matawale ya yi tsakanin Fulani da ‘Yan sana kai da  ‘Yan banga ,ya sanya yanzu haka Mutane Sama da dari hudu da arba’in ne ya amso daga hannun masu garkuwa da mutane a fadin jiahr ta Zamfara.

Wasu mutanan sun fitone daga Jihohin Kaduna da Katsina da Sokoto da Neja kuma tuni suka koma wajajan iyalansu.

Haka nan, yanzu haka garuruwa sama da dari biyu da al’ummar suka kaurace masu su kai gudun hijira zuwa garuruwan jihar da ma wajan jihar sun koma gidajansu lami lafiya .

Wadannan manyan nasarorin da Matawale ya samu ya sanya duk garin da ya ratsa babu abin da ake masa sai addu’a da fatan alherin ga gwamnatinsa .

Haka kazali, samun babbar nasarar tsaro ya sanya Gwamna Matawale shirya gagarimin wasan Fulani na sallah, wanda ba a tabayin irinsa ba a fadin jihar ta Zamfara inda Fulani sukai shagulgulan Sallah a duk fadin kananan hukumomin jihar wanda wannan bikin ya kara jawo ma al’ummar jihar bakin ‘yan kasuwa da suka kaurace ma jihar shekara da shekaru.

Bangaren ma’aikata kuwa cikin Kawana dari da gwamnatin Malawale ta yi sun samu kudin Hutu da shekaru takwas suka rasa shi. Gwamnan ya ba Ma’aikata kudin hutu da albashinsu inda aka yi has ashen wannan ya sa dabobi su kai tashin gwauran zabi sakamakon samun kudi ga ma’aikatan jihar baki daya .

A kokarin samun dauwamamen zaman lafiya da kuma killace Fulani a guri daya dan su ma su amfana da roman damakwaradiya, a ranar Labaran nan Gwamnan matawale ya sanya Harsashin gina Ruga ta Zamani a yankunan ‘Yan majalisar datawa uku da a ke dasu a fadin jihar .

Za a  gina masu gidaje dari biyar da asibiti da makarantun boko da na Islamiya da kuma ofishin ‘Yan sanda da kuma gina masu madatsar ruwa da wajan kiwo da wurin shuka ciyawa, inda za a rika samar da madarar shanu mai inganci da tsafta.

An fara sanya tubalin gina rugar ne cikin Karamar Hukumar Maradun da kuma Dan sadau a cikin Karamar hukumar Maru da kuma Gidan jaja a cikin karamar hukumar Zurmi .

Wadannan shirin na samar da Ruga da amso mutane daga hannun masu garkuwa da mutane da mai da ‘yan gudun hijira gidajansu,da samar da tsaro shi ne ginshikin bikin cika kwana dari da mulkin Gwamna Bello Muhammad Matawale.

  Sai dai kuma, abin da al’umma ke bukatar Gwamna Bello Matawale ya maida hanakili a kai shi ne Farfado da harkar kasuwanci a fadin jihar ta Zamfara.

Kuma ga alamu ya fara, domin a duk ayyukan da Gwamnatin ta ba da, ta hana ‘yan kwagila fita wajen jihar dan sawo kayan aiki, duk abin da dan kwangila zai yi amfani da shi dole ne ya saye shi a cikin jihar kuma hatta lebira da masu aikin, bai aminta da a dauko wani dan wata jihar ba sai ‘yan jihar Zamfara, kuma wannan ne zai taimaka wajan samar wa jama’a abin yi da kuma yaki da zaman banza a fadin jihar ta zamfara.

Zunubai 12 Da Gwamnan Nasarawa Ya Kawar Da Su Cikin Kwanaki 100

Daga Zubairu T.M.Lawal

Tum bayan da aka rantsar da Injiniya Abdullahi Sule a kan karagar kujerar Gwamnan jihar Nasarawa, a ranar 29/5/2019 Gwamnan ya yi alkawarin samar da sauye-sauye masu  inganci ga al’umman Jihar.

Musamman matsalolin da al’umman Jihar suke fama da shi kama daga Ma’aikata zuwa masu bukatar aiki da kuma harkokin more rayuwa na ci gaban Jihar.

A ranar da aka rantsar da Gwamnan ya yi alkawarin taimakawa mata da matasa da kayan sana’ar hannu cikin awa 48 duk da cewa wannan alkawarin akwai hadin gwiwa da tsakanin hukumar tallafi ta tashar jiragen ruwa ta kasa. Amma Gwamnan ya cika alkawarin da ya dauka an kuma raba injunan Nika da sauransu.

Batun Albashi

Game da batun albashin ma’aikata da Gwamnan ya tarar da wannan matsalolin, yadda ake biyan Ma’aikata albashi rabi da rabi, ko kwata-kwata . Gwamna Abdullah Sule ya kawar da wannan lamarin, yanzun ma’aikatan Jihar Nasarawa suna karban albashi kashi dari bisa dari.100% a kowane wata.

Wannan ya sanya batun rigima tsakanin ma’aikatan Gwamnati da bangaren mahukunta aka samu saukin lamarin babu ta da jijiyar wuya.

Zuwa Aiki

Cikin manyan ayyukan ci gaba da Gwamnan ya samar da su, yanzu ya sanya ido a kan Ma’aikatan Gwamnatin jihar, kowa na zuwa aiki a kan lokaci ya kuma tashi a kan lokaci.

Sakamakon zagayen da Gwamnan yake yi zuwa Ma’aikatun Gwamnati da sanyin safiya. Gwamnan ya dauki matakin ba sani, ba sabo, a kan duk ma’aikacin da ba ya fitowa aiki a kan lokaci.

Karin Girma

Haka-zalika batun karin girma da Ma’aikatan jihar  suka kwashe tsawon shekaru takwas suna zaune guri daya babu gaba, babu baya, Ma’aikaci yana matsayi daya. Cikin kwanaki dari na Injiniya Abdullahi Sule, ya nuna rashin amincewarsa da wannan kudurin.

Fansho

Akwai babban matsala da Gwamnan Abdullahi Sule, ya tarar da ita tsakanin tsaffin Ma’aikata da Gwamnatin jihar, wanda lamarin har ta kai ga zuwa kotu. Fanshoniya sun maka Gwamnatin Jihar Nasarawa a wata Babban kotu da ke garin makurdi a jihar Benuwe sakamakon rashin biyan su hakkokinsu na Fansho, wanda ta sanadiyyar haka suka fada cikin matsalolin rayuwa.

Ta kai ga Kungiyoyin Fanshoniya sun rika gudanar da zanga-zanga suna nunawa duniya halin da suke ciki na rashin biyansu hakkokinsu ta kai su ga mutuwa da kwanciya rashin lafiya.

Yanzu dai Gwamna Abdullahi Sule, ya warware bakin zaren yana biyansu hakkokkinsu 100%.

Matasa

Gwamnatin Jihar ta dukufa wajen taimakawa kungiyoyin matasa da ayyukan yi na hannu. Gwamnatin tana hada gamayyar kungiyoyi na matasa maza da mata ta koyar da su sana’ar hannu. Cikin wannan makon Gwamnatin ta sallami matasa 262 wadanda aka koyar da su sana’ar buga jan Bulo na zamani, kuma aka samar masu da injunan buga bulo wanda za su yi ayyukansu da shi.

Baya ga injunan nika da injunan saka da Gwamnatin ta rabawa Matasa a farkon hawanta.

Fannin Ilimi

Gwamnan ya farfado da ayyukan gina dakunan karatu a kananan makarantu daga Firamare zuwa kananan Sakandire tare da samar da ruwan sha mai tsafta a cikin Makarantu.

Wannan ayyukan ya karfafata su ne ta bangaren Muradun ci gaban karni, wato (SDG). Za a gina dakunan karatu da bayan gida da ruwan sha da kuma ofisoshin Malamai.

A baya jihar tana fama da karancin dakunan karatu sakamakon maida makarantun Gwamnati zuwa wasu makarantun na dabam.

Akwai babban burin ganin ilimi ya inganta a jihar tare da ganin ‘ya’yan talakawa suna cin moriyar wannan tallafin na ilimi.

Gwamna Abdullahi Sule, ya bayyana cewa akwai shirin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin jihar da wani kamfani, yadda za a zakulo yaran da suka fi kowa hazaka a makarantu domin ba su tallafin zuwa karatu a kasashen waje.

Lantarki

Yanzu Gwamnati ta fara sanya wutan lantarki na kan hanya a dukkan kananan hukumomi goma sha uku da ke fadin jihar.

Gwamnatin ta tabbatar da fara sanayawa kowace karamar hukuma za a sanya wutan kan hanya na tsawon kilomita biyu.

Kamun Ludayin Sabbin Gwamnonin Arewa A Cikin Kwana 100 Na Mulki

Gwamnatin jihar Nasarawa ta farfado da tsare-tsaren tsaftace muhalli a dukkan fadin jihar.

Yanzu ana tsara yadda za a inganta harkokin shara a dukkanin jihar. Kuma Gwamnati ta tsara yadda za ta karrama karamar hukumar da aka samu tafi tsafta a jihar, za a ba ta lambar yabo. Wannan zai zama gasa na dukkanin wata a ga wata karamar hukumace ta fi tsafta.

Sannan za a hukunta duk karamar hukumar da aka samu da barin kazanta a cikin ta.

Tsaro

Gwamnan ya dukufa wajen ganin an samu ingantaccen tsaro a jihar Nasarawa saboda jihar tana fama da irin matsalolin ayyukan Ta’danci da kai hare-haren da masu garkuwa da mutane.

Wannan yana daya daga cikin matsalolin da yake ci wa al’umman jihar tuwo a kwarya.

Duk da haka, Gwamnan yana iya bakin kokarinsa wajen ganin al’umman jihar sun samu zaman lafiya musamman ga junansu, saboda rikicin cikin gida kamar Manoma da makiyaya.

Hanyoyi

Gwamna Abdullahi Sule, ya kaddamar da gina hanyoyi tare da magudanan ruwa sakamakon ambaliyan ruwa da yake janyo zaizayar kasa , wanda a duk shekara ke janyo asara mai yawa.

Gwamnatin tana gina manyan magudanan ruwa a cikin gari da sauran gurare.

Batun Albarkatun Kasa

Gwamnatin ta sanya shirin neman albarkatun kasa a fadin jihar. Wanda zai taimaka mata wajen samar da ayyukan yi ga al’umman jihar da kuma hanyoyin kudaden shiga.

Bangaren Noma

Game da harkar noma, Gwamnatin jihar Nasarawa ta farfado da harkan noma yadda ta samar da takin zamani ga manoma a kan farashi mai sauki. A wannan shekarar Gwamnati ta rabawa manoma takin zamani kan farashin naira dubu uku da dari biyar kowane Buhu.

Gwamnatin ta dauki matakin ganin manomane kawai suka samu wannan takin ba su yarda a yi harkan kasuwanci da shi ba. Kuma ba su amince da a fita da takin zuwa wajen jihar ba.

Sannan Gwamnatin ta karfafawa manoma gwiwa wajen samar da irin da za ayi amfani da shi a gona. Haka-zalika ta tabbatar da tsaron lafiyan manoma yayin da suke aiki a gonakansu.

Gwamnatin Jihar Adamawa Kan Sikeli Cikin Kwana 100

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Yanzu da gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ke cika kwanaki dari kan karagar mulki, ko wadanne nasarori gwamnan ya samu? Domin neman amsar wannan tambayar LEADERSHIP AYAU JUMA’A, ta shiga gari inda jama’ar jihar suka bayyana ra’ayoyi mabambanta a kai.

In da da dama ke bayyana gwamnatin da cewa ta yi rawar gani, domin kuwa a cewar su gwamnatin ta shawo kan matsalar kungiyoyin matasa ‘yan shila da ke kwace wayoyi da jakunkunan mata, da kuma sukan mutane da wukake.

Alhaji Abdullahi Rabo, mataimakin shugaban kungiyar direbobin tanka ta kasa, shiyyar arewacin Nijeriya ya ce, “duk da kwanaki 100 sun yi kadan a yanke hukunci ga gwamnati, amma mun ga abubuwan ci gaba ta bangaren biyan kudin albashin ma’aikata.

“Kuma gwamna ya ki ya nada kwamishinoni, mun ji an ce saboda ya rage yawan kudaden garatuti da fenshon da tsaffin ma’aikata suke bi ne, to wannan abu ne mai kyau, mun ji kuma a watan sha daya zai dauke biyan kudin makaranta ga iyaye.

“Yanzu ana biyan albashi tun 23 ga wata, wannan ko gwamnatin tarayya ba ta cika yin haka ba, muna yi wa wannan gwamnati addu’a Allah ya ba ta ikon cika alkawuran da ta yi wa jama’a, amma mun gani a kasa cikin kwanaki darin gwamna Fintiri.

“abin da muke son gani shi ne ya nada kwamishinoni, domin yanzu ayyukan gwamnati kamar aikin hanya, da wasu ayyuka sun tsaya, amma idan ya nada kwamishinoni aiki zai rika tafiya komi na gwamnati zai tafi daidai” in ji Rabo.

Awwal Muhammad, wani dan siyasa, ya ce “Alhamdulillahi muna yi wa Allah godiya da ya nuna mana wadannan kwanaki dari na sabuwar gwamnati a jihar Adamawa, na biyu kuma mun ga canji ta yadda ma’aikatanmu suna samun albashi a kan lokaci, don yanzu albashi ba alfarma ba ne hakki ne.

“Domin ina tabbatar maka yanzu wata biyu kenan gwamna na biyan albashi ranar 23 ga wata, to mun ga ci gaba sosai ta wannan bangare, kuma an samu ci gaba ta matsalar tsaro, da Jimeta akwai yaran da muke fama da su shekaru biyu wadanda ake musu lakabi da ‘yan Shila.

“To Alhamdulillahi ba za mu ce gaba-daya sun kau ba, amma mun samu saukin faruwan matsalarsu, idan da za ka samu labarin an kwace waya ko an kwace jaka sau biyar-shida to yanzu da wuya ka ji sau daya a yini, za a iya yin sati kafin ka ji anyi guda biyu.

“Abu na uku shi ne, akwai ikrarin da shi mai girma gwamna ya yi na cewa daga watan taran da muka shiga, na sabon zangon karatun da za mu shiga, zai zama iyaye za su daina biyan kudin makaranta daga Firamare da Sakandire, har zuwa biyan kudin jarabawar WEAC da NECO, wannan ba karamin ci gaba aka samu ba” in ji Awwal.

Haka shi ma shugaban bangaren sadarwar gwamnan, Solomon Kumangar, ya ce “idan kana jihar Adamawa kafin mai girma gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya dare karagar mulki ka san akwai matsaloli da kura-kurai a harkar gudanar da gwamnati, musamman ta fuskar tsaro.

“jama’a na fama da matsalar ‘yan shila da masu garkuwa da mutane, amma da zuwan sa shi mai girma gwamna ya dakile matsalar, yanzu ba a jin batun ‘yan shila ba a kuma jin batun garkuwa da mutane, ko da shike ba a ce an gama gaba-daya ba, amma idan aka yi la’akari da abubuwan da yake faruwa a kwanan baya za a ce lallai an samu ci gaba.

“Baya ga haka, akwai samar da abinci mai inganci ga yara da suke makarantun kwana na gwamnati, sannan kuma a watan Satumba lokacin da za a dawo makaranta mai girma gwamna ya ce duk makarantun Adamawa ba za a sake biyan kudin makaranta ba, kuma ya zama tilas ga yaron da ya kai shekarar shiga firamare, iyaye su tura shi makaranta.

“Akwai kuma shirin da akayi na samar da gidaje ga ma’aikata wanda ya rattaba hannu kwanan nan da wani kamfani na gwamnatin tarayya wanda gwamnatin tarayyar ne za ta ba da kudi, shi ma zai ba da kashi 40, ina ganin sati mai zuwa za a fara wannan aikin” in ji Kumangar.

Da yake magana game da bunkasa harkar noma kuwa, Solomon Kumangar ya ce cikin kwanaki darin ne gwamnan ya samar da taraktoci 150, domin bunkasa noma, ya ce “wadannan abubuwa ne kalilan da zamu iya mu bugi kirji a kai, wadannan mai girma gwamna ya riga da ya aiwatar da su cikin kwanaki 100” in ji Kumangar.

Kwanaki 100 Na Gwamna Inuwa Yahaya, Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kasance zababben gwamnan farar hula na hudu a jihar, wanda a kwanaki dari na farkon mulkin sa ya yi rawar ganin da a sauran gwamnonin da aka yi a baya ba a samu irin wannan kwazo na Gwamna Inuwa Yahaya ba.

Alhaji Inuwa Yahaya, kafin ya zama gwamna a jihar Gombe, ya yi takara a shekarar 2015 Allah bai ba shi nasara ba, sai a shekarar 2019 inda ya samu nasara kuma ya ka da dan takarar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, na jam’iyyar PDP, Sanata Usman Bayero Nafada, shi kuma tsohon gwamnan ya fadi a zaben sa na Sanata a yankin Gombe ta arewa.

Daga hawan sa kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu a jawabin sa na karbar mulki a filin wasa na Unguwar Pantami da ke fadar jihar, ya yi alkawarin kawo wa jihar abubuwan ci gaba da kuma kawo karshen aika-aikar matasa na ta’addanci, sannan kuma ya ce kafin kwanakin sa dari na farko a mulki zai yi wasu ayyukan ci gaba masu ma’ana a jihar.

Alhaji Inuwa Yahaya, ya fara da gyaran ruwan famfo a fadin jihar, inda ya ware zunzurutun kudi naira miliyan dari da takwas wajen ganin an gyara dukkan wasu fayel-fayel na ruwa da suka lalace sannan a kuma kara yawan ruwan da ake bai wa jama’a a jihar daga matatar ruwa na dam din Dadin-kowa.

Wannan aikin gyaran ruwa yana tafiya ne ta karkashin kwamitin da gwamnan ya kafa bisa jagorancin tsohon babban sakataren ma’aikatar ayyuka na jihar, Injiniya Abubakar Bappah, wanda kuma shi ne mai rikon hukumar samar da ruwan ta water board.

Bayan ga aikin ruwa, yanzun haka, Gwamna Inuwa Yahaya ya ba da aikin wasu hanyoyi da ake gudanarwa a Unguwar Jekadafari da ke fadar jihar da kuma Unguwannin Malama Inna da Arawa da Kagarawal da Wuro-Kesa har ta wuce Kurba a yankin karamar hukumar Yamaltu Deba da za ta lashe kudi zunzurutu har naira biliyan daya da miliayan dari shida 1.6 billion.

Sannan ya bayar da aikin hanya a garin Billiri da ta tashi daga Kulkul ta wuce har zuwa Ayaba mai tsawon kilomita shida da ita ma za ta ci kudi masu yawa da yanzu haka aikin ta ya yi nisa sosai.

Gwamna Inuwa Yahaya, mutum ne mai kishin jihar sa domin babban abun da ya sa ya jajirce sai ya zama gwamna a jihar shi ne saboda kawo gyara wanda ya jima yana son ba da tasa gudumawar wajen ganin jihar Gombe ta kara zama sahun zama a tsakanin jihohin arewa maso gabas.

A wannan rana ta Juma’a da ake bikin cikar sa kwanaki dari a kujerar mulki duk wani dan Gombe ya san Inuwa Yahaya ya kamanta wajen gudanar da ayyuka daidai gwargwado a jihar, ba kuma iya fadar jihar Gombe kadai yake yi wa aiki ba duk yankunan karkara ya hada domin ko da hanyoyi da ake yi sun fi yawa a yankunan karkara.

Yanzun haka ma ganin Motocin sufuri na Gombe Line sun mutu ya shirya kawo wasu sababbi fil a leda inda yanzu haka tuni guda hamsi sun iso jihar a karon farko da za a nunawa mutane a ranar bikin cikar kwanaki dari sauran na biye nan ba da jimawa ba.

Alhaji Inuwa Yahaya, ya kasance gwamna da bai jin gulmace-gulmace na ‘yan siyasa wanda hakan ne ma ya sa duk inda ya kamata a yi wa aiki yakan tura a duba ya kuma yi ba tare da nuna bambanci ba saboda ganin ai cewa Gombe duk Gombe ce, duk inda aka yi wa aikin a Gombe aka yi ba a wata jiha daban ba.

Ganin hakan ne ya sa al’ummar Gombe suke masa wani kirari da, Inuwa gida-gida domin alherin sa ya ratsa ko’ina a jihar duk wani gida indai a Gombe yake tun daga lokacin yakin  neman zaben sa har ya zama gwamna zuwa yanzu an shaida ribar mulkin Inuwa Yahaya.

Alkawarin da Inuwa Yahaya ya yi na samar wa da matasan jihar aikin yi ya fara domin a bikin kaddamar da dashen itatuwa Miliyan hudu da ya yi ya tabbatar da daukar Mata da Matasa guda dubu 25 da za su dinga kula da wadanan itatuwa inda kowanne za a dinga biyan su duk wata.

Sannan kuma ya kara da bayyana cewa, don ganin an daina zaman banza da kuma ganin rayuwa ta inganta ya sa ya ba da umurnin sanya kowane Yaro a Makaranta da yin ilimin zamani kuma kyauta inda ya ce duk wani Uba da bai sanya dansa ko ‘Yarsa a Makaranta ba za a hukunta shi domin idan da talauci ya yi tasiri wajen hana sanya ‘Ya’ya a Makaranta to yanzu an maida shi kyauta kuma dole.

Wasu jama’a da suka bayyana ra’ayoyin su kan bikin wannan rana, wasu sun yaba wasu kuma sun ce da gyara, inda Alhaji Mani Adamu ya shaida cewa Inuwa ya dasa Itatuwa a gari ba shi ne bukatar mutanen Gombe ba, kamata ya yi ya magance musu yunwa da fatara da ake ciki sannan ya hada kai da gwamnatin tarayya a magance kwarurrukan da suka addabi jihar Gombe musamman daga gidan Dan Gusau zuwa hayin kwarin Misau, inda Jama’a suke rasa gidajen su sakamakon zaizayewar kwari.

Shi kuma Aliyu Umar, cewa ya yi yanzu aka samu gwamna a Gombe wanda ya san daraja da mutuncin mutane domin a baya an yi gwamnati marar albarka yanzu aka samu gwamna a Gombe.

Ya kuma ce koma dai ya ya ne, Inuwa Yahaya zai cire musu kitse a wuta wajen ganin ya gina jihar domin tun daga yanzu a kwanaki darinsa na  farkon nan ‘yar manuniya ta nuna cewa zai yi aiki saboda ya fara an gani kuma ayyukan da suka shafi talaka kai tsaye yake yi.

Aliyu Umar, ya ci gaba da cewa, duk mai cewa Inuwa Yahaya ba abin da ya yi a kwana darin nan, to gaskiya dan adawa ne wanda kuma ba yadda za a yi dama a yi siyasa ko gwamnati ba tare da adawa ba, don haka su jama’ar jihar Gombe da suka zabe shi sun san mai kishin kasa ne, kuma mai kaunar ci gaban jihar Gombe da al’ummar ta ne.          

Jihohin Borno Da Yobe

Gwamna Zulum Na Jihar Borno

Gwamna Mai Mala Buni Na Jihar Yobe

Kowa ya san bisa irin yadda rikicin book haram ya yi barna a yankin arewa ta gabas, musamman Borno da Yobe, babban abin da gwamnonin jihohin biyu, Gwamna Zullum da Mai Mala Buni suka tasa a gaba shi ne farfado da yankunan jihohin nasu da suka fi ta gayyara.

Wakilinmu ya bayyana mana cewa, yanzu haka Gwamna Zullum ya dukufa wajen ganin ‘yan gudun hijira sun koma yankunansu na asali. Sannan ya kara kaimi wajen bunkasa sha’anin ilimi daga inda Gwamna Kashin Shettima da ya gada ya tsaya.

Haka nan a jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kara himmar sake gina yankunan da rikicin book haram ya ruguza, inda a kwanan nan y aba da wata katafariyar kwangilar gina gidaje a fadin jihar.

Haka nan shi ma, ya mayar da hankali sosai a kan batun kiwon lafiya da sha’anin ilimi na al’ummar jihar.

LEADERSHIP A YAU dai za ta ci gaba da kawo muku nasarorin da sababbin gwamnonin suka samar a jaridunmu na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!