Connect with us

Da dimi-diminsa

Kwana 100 A Ofis: Dr. Dauda Lawal Ya Yaba Da Salon Gwamna Matawalle

Published

on

Tsohon Shugaban Banki, shahararren masanin tattalin arziki, kuma gogaggen dan siyasar nan, Dakta Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau) ya yi yabo ga kamun ludayin Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle a yayin da gwamnan ya cika kwana 100 a ofis.

Dakta Dauda ya kwatanta Gwamna Matawalle a matsayin wani jajirtacce, kuma tsayayyen mutum, wanda ya tsamo Jihar Zamfara daga mawuyacin halin da gwamnatocin baya suka jefa ta ciki.

Wadannan bayanai na Dakta Dauda Lawal sun fito ne a wata takardar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, a ka kuma rabawa ‘yan jarida.

Dakta Dauda Lawal ya ce, kwanaki 100 na Gwamna Matawalle a ofis sun zo da alherai masu tarin yawa.

Ya ce: “A yau ne Gwamna Matawalle ke cika kwana 100 a ofis, a matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara. Tabbas a cikin wadannan kwanaki 100, Gwamna Bello ya ba marar da kunya. Ya zo a daidai lokacin da jihar ke matukar bukatarsa, sannan kuma ya dora gwamnatinsa kan yin daidai.

“Idan a ka kalli yadda ya saisaita al’amarin tsaro a fadin Jihar Zamfara kawai ya isa a gode wa Allah. Domin a ‘yan watannin baya lokacin waccan tsohuwar gwamnatin, Zamfara na daga cikin wurare mafi hadari a Nijeriya, amma a yau labarin ya canza, zaman lafiya ya samu.

“Idan ka duba fannin ilimi ma, sabuwar gwamnatin ta yi kokari matuka, domin an farfado da martabar malamai, da makarantu a fadin Jihar.”

Daga karshe, Dakta Dauda ya yi kira ga gwamna Matawalle da ya ci gaba da yin aiki tukuru don ganin Jihar Zamfara ta daukaka.

“Tun farko da ma burinmu shi ne ganin ci gaban Jihar Zamfara, wannan ne ma ya sa muka yi tsayin daka, tare da kalubalantar karfa-karfar kafa gwamnati wanda tsohuwar gwamnati ta so ta yi. Tunda wannan gwamnatin ta zo, kuma muka fahimci tana da kyakkyawan manufa, shi ya sa muke goyon bayanta, muke kuma yi mata fatan alheri.”

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: