Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sharhi:Kyawun Alkawari Cikawa

Published

on

A yayin da kasar Sin ke ci gaba da daukar matakan da suka dace na kara bude kofarta ga ketare, a hannu guda kuma wasu kasashen yamma makiya ci gaban kasar na kokarin kawo wa kasar baraka, amma burinsu ba zai ci nasara ba.

Matakan bude kofar kasar ta Sin, sun kunshi sassauta dokoki da ka’idojin zuba jari ga baki ’yan kasuwa masu sha’awar zuba jari a cikin kasar, da kara fadada sassan zuba jari da samar da muhallin zuba jari mai inganci shi kansa. Hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama na zamani masu inganci, na daga cikin abubuwan da za su karo janyo hankulan baki masu sha’awar zuba jari a cikin kasar.
Kammala gwajin tashi da saukar jiragen sama a filin jiragen sama na Jieyang Chaoshan dake yankin kudancin Sin, wani bangare ne na matakan mahukuntan kasar da zai saukakawa baki masu sha’awar zuba jari a cikin kasar.
Yanzu haka, filin jirgin yana iya karbar manyan jiragen sama samfurin Boeing 787, da Airbus 330. Yana kuma baiwa fasinjoji damar tashi zuwa sassan nahiyar Turai da Amurka, an kuma fadada harabar dake karbar jirage 21 zuwa 40.
Masu iya magana na cewa,kyawun alkawari cikawa, wannan ya kara tabbatar da aniyyar kasar Sin na bude kofarta ga ketare ta yadda za a gudu tare a tsira tare. Burin kasar Sin a kullum shi ne samar da damammakin zuba jari ga kamfanoni na kasa da kasa, da zakulo hanyoyin inganta muhallin zuba jari, cikin adalci, ba tare da wata rufa-rufa ba.
Yanzu haka, akwai kimanin manyan kamfanoni sama da 400, cikin kamfanoni mafiya girma 500 dake sassan duniya da suka zuba jari a kasar Sin. Wani batu na baya-bayan nan, shi ne kudurin kasar na kara kafa yankunan cinikayya maras shinge na gwaji a larduna 6 na kasar, adadin da yanzu irin wadannan yankuna ya tashi zuwa 18. “Kyakkyawar Jumma’a tun daga Laraba ake gane ta.” (Ibrahim Yaya)
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: