Connect with us

TASKIRA

Yadda Za Ki Yi Idan Mijinki Ya Yi Miki Laifi Kuma Ya Kama Fada A Kai

Published

on

Idan mijinka yayi maka abinda ranka ya baci sosai. Kuma shine mara gaskiya dan kuwa macen bata da laifi ko kadan. Se kuma yayi ta fada, ya ma dena mata magana. Ko kiranta ba yayi bare ya daga wayarta idan ita ta kira. Tambaya: Me ya kamata ta yi? Shin za ta bashi hakuri ne ita ta dauki laifin ko kuwa a`a, za ta nuna masa abin da ya yi ba daidai ba ne, kuma ta yaya za ta yi hakan?

Amsa:

A gaskiya ya danganta. Kuma akawai dubaru da dama da zata iya amfani da shi.  Na daya dai idan mazauni ne toh ga shawara: Abunda ya fi komai mahimmanci a kokarin sasanta ko wani irin sabani ko neman sulhu shi ne ‘approach’. Duk da shi ke da laifi ya kamata ki fara tunkararsa ta hanyar da za ki daure shi da jiniyoyin jikin shi dan ki samu abunda kike so.

Bayan dan lokaci kadan in hankali ya kwanta. Ko da daddaren ranan da abun ya faru ko washegari, se i bukaci magana da shi a lokacin da shi ya shirya kuma yana da daman haka. Ma’anakice mishi Dan Allah kina bukatar magana da shi a duk sadda ya shirya ko yake da lokaci. Idan ya amince kuka samu wuri kuka zauna a tsanaki, abu na farko da za ki fara yi shi ne yabon halayen sa na kirki, sannan ki godewa abubun alheri da yakan yi muku ke da yara, domin kuwa idan Manzon Allah Sallallahu alaihi wa Sallam ze yi gyara ko wani iri ne da haka yake farawa.

Na biyu: cikin ladabi da biyayya da murya me laushi ki fada masa ba ki ji dadin abunda ya faru dazu ba, idan an zauna tattaunawa da yamman ranan kenan. Ko jiya idan washe gari ne, se ki tsaya a nan. Kar ki fara da cewa ai ba ka kyauta ba ko kuma ba ka da kirki ko kuma dan me ya sa ka yi mun kaza da kaza.

Idan kika fara da daya daga cikin abubuwa ukun nan dana lissafi a sama, toh a karshen ina me tabbatar miki da cewa ba za ki taba samun yadda kike so ba.

Amma idan kika isar da sakon ki ki yi shiru ki ji me zai ce. Idan ya yi kokarin cewa ai ke ce kika yi kaza shiya sa na yi kaza. Sannan a cikin murya me dadi da ladabi da biyayya kice haba wane, da ba sai ka kira ni ka zaunar da ni kamar irin haka ka ji daga gareni ba, ko kuma idan laifi na yi maka ka sanar da ni kari da yi mun nasiha maimakon ka yi mun haka? Ai ya fi dadi da mutunci. Ki tabbatar cewa babu gardama dan ba ita kuka zo yi ba. Magana za ku yi na hankali cikin ruwan sanyi babu daga jijiyan wuya.

Idan ba mazauni ba ne misali a waya ne. Toh ga shawara: In ya ki daukan wayan ki, ki aika mishi da rubutaccen sako. Idan be amsa ki ba ki aika mishi da sakon murya. Kar da ki yi magana a kan abin da ya faru tun da baya son ji. Gasuwa kawai da kalamen soyayya za kiyi ta aikawa har sai kin shawo kan shi kin samu ya aiko da amsa kun fara magana. Sadda kuke cikin farin ciki da nishadi ko wasa ki ce Dan Allah akwai abun da kike so ki fada mishi kuma kina rokon shi da ya baki hadin kai. Se ki shigo da zancen kamar yana nan yadda muka fada a sama. Cikin tattausar murya farawa da halaye da ababen kirki da yakan yi. Ki tabbatar cewa babu gardama. Tattaunawa na hankali za ku yi.

A karshe ki tambaye shi wane; Dan Allah kana so na? Dan Allah kana sha’awar zama me dadi cikin kwanciyar hankali da natsuwa? Kana sha’awar zama me cike da nishadi da annashuwa? Na tabbata ze ce miki eh duk yana sha’awan wadannan ababe da kika tambaya. Ki ce mishi kema su kike sha’awa saboda haka Dan Allah Dan son Annabi kina so ku taimaka ma juna ku ga cewa kun samu hakan ta hanyar dena hantaran juna ko da an samu sabani. Ku yi kokari ku dinga yin zama irin wannan na mutunci da hankali domin samun maslaha cikin sauki. Kuma wannan abun da ya yi miki ya yi miki ciwo sosai Dan Allah kar ya kuma yi miki hakan. Cikin tattausar murya ne za ki fada masa idan ya sake yi miki irin haka gaskiya ba zaki sake cin abinci ba don za ki tafi yajin aikin cin abinci (hunger strike) ko kuma wani abu da kika san yana tada masa hankali.

A karshe, kina iya gudun bacin rai ta hanyan maida fadansa wasa. Duk sadda ya tumkaro ki yana farawa tun kafin ya yi nisa sai ki dauke mishi hankali ta hanyar fadar wasu kalamai na shagwaba ko ki maida shi yaro kawai ki ruga da gudu kice in ze iya ya biyo ko ki yi mishi gwalo ko dai wani abu makamancin haka.

Allah Ubangiji ya cigaba da dafa mana duniya da lahira baki daya in sha Allah.

Binta Shehu Bamalli

Mrs Mustapha L S
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: