Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Yunkurin Ta Da Zaune Tsaye A Hongkong Ba Zai Cimma Nasara Ba

Published

on

Wasu masu bore suna neman kawo baraka a yankin Hongkong, ta hanyar tarzoman da suka tayar kwanan baya bisa goyon bayan da asusun NED na Amurka ya ba su.

Kafar yada labarai ta Hongkong ta bayyana cewa, tun daga shekarar 1995, wannan asusu ya fara tallafawa ’yan adawa ta yankin har zuwa farkon shekarar 2015, inda yawan kudin da ya samar musu ya kai dala miliyan 3.95.

To sai dai kuma duk da hakan, ba wanda zai cimma nasarar juyin mulki a yankin Hongkong, kana Sin ba za ta yarda da duk wani matakin dake kawo barazana ga ikon mulkin kasar, da ikon gwamnatin tsakiya, da dokar musamman ta Hongkong ba, balle a yi amfani da Hongkong don kawo barazana ga babban yankin kasar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: