Connect with us

TATTAUNAWA

Babban Abin Jin Dadi A Rayuwa Ka Zama Abin Koyi Ga Na Baya —Farfesa Sani

Published

on

Gabatarwa

Sunanan Farffesa Sani Ibrahin Fagge, malami a Sashin nazarin sinadaran rayuwa(Biochemistry) da ke jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Na yi makarantar Firamare a garin Bienin Kudu wadda ke jihar jigawa a halin yanzu. Ban gama ba sai muka dawo Kano inda na ci gaba da karatuna makarantar Kurna wanda kuma na gama a nan.

Bayan kammala Firamaren tawa, sai na tafi Gwarzo inda na yi sakandire daga nan na samu nasarar shiga makarantar share fagen shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Dagan an na ci gaba da karatuna a jami’ar  a sashin nazarin kimiyyar sinadaran rayuwa. Bayan n agama digina na farko a wannan fanni na je na yi hidimar kasata a Legas a sheka ta 1980.

Bayan kammala wannan hidimar kasa a shekara ta 1981, sai malamaina suka bukaci in dawo in ci gaba da karatu a nan jami’ar ta Ahmadu Bello. Saboda haka a nan na yi karatun digirina na biyu.

Bayan na gama karatun dirina na biyu sai na tafi kasar Ingila inda a nan na yi digirin digirgir wato digi na uku. Bayan kammala wannan karatunawa a Ingila sai na sake dawowa jami’ar Ahmadu Bello inda na ci gaba da gashi a fannin da rubuce-rubuce.

Cikin ikon Allah na fara aiki a jami’ar Ahmadu Bello a matsayin ma fi kankantar malamin makaranta har zuwa wannan matsayi da ke a yanzu na babban malamin jami’a. Na samu nasarar zama Farfesa tun kimanin shekara goma da suka wuce.

Kalubalen Da Na Fuskanta  A Rayuwa

Alhamdu lillahi, duk da cewa, rayuwa tattare take da kalubale, amma ni zan iya cewa, na samu saukin kalubalen rayuwa, musamman da yake ma fi yawancin rayuwata ta tafi a akan koyo da koyarwa, kuma Allah ya ba ni basirar fahimtar karatu, saboda haka duk inda na fuskanci jarabawa nakan samu nasara, sannan kuma ga cikakken goyan baya da nake samu daga mahaifana. Sai dai kawai dan kalubalen da na fuskanta bai wuce lokacin da nake karau a Kurna kafin a saya min keke, na kan taka a kafa daga Fagge zuwa Kurna.

Bayan wannan kuma lokacin da muka je Gwarzo babbar matsalarmu a wannan lokaci ita ce, ta ruwan sha, ta kai wani lokacin bayan ka je ka debo ruwan sai ka tace da kyalle kafin ka sha. Saboda haka zan iya cewa, in ma kwai wadansu kalubale da na fuskanta a rayuta musamman ta karatu ba su wuce wadannan ba.

Nasarorin Da Na Samu Rayuwa

Babban nasarar da na samu a rayuta ita ce, na farko, Allah ya azurtani da iyayen da suka gina min rayuwa a kan ilimi ta hanyar ba ni dukkan kulawar da ta kamata na ganin cewa na yi ilimin addini da na zami da kuma kuma dorani a kan kyakkyawar tarbiyya.

Nasarata ta biyu, ita bayan wannan goyon baya da na samu, Allah kuma ya azurtani da kwakwalwar fahimtar dukkan abin da aka koya min, wanda wannan kuma ya kara karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da ba ni goyon bayan karatuna.

Haka kuma na samu nasarar bayar da gudummowar bunkasa wannan Sashi na nazarin kimiyyar sindaran rayuwa ta hanyar jawo wasu mutane da a yanzu suke bayar da cikakkiyar gudummowa wajen kara habaka wannan Sashi.     

Sannan a matsayina na malamin jami’a da na shafe shekaru masu yawa ina koyar da dalibai, ina jin dadi tare da alfaharin cewa, na koyar da mtanen da ban san adadinsu ba wadanda suka samu ci gaba a rayuwarsu sannan kuma suke bayar da gudummowa wajen bunkasa kasa da rayuwar al’umma.

Burina A Rayuwa

Babban burina a rayuwa, shi ne in gama lafiya da samun zuri’a ta gari wadda za ta taimaki kanta da sauran al’umma, sannan kuma ina da burin in ga matasanmu sun rungumi ilimin addini da na zamani kuma sun samu kyakkywar tarbiyya. Haka kuma ina da sha’awar jin cewa, dukkan daliban da na koyar sun samu hanyar dogaro da kai da kuma tallafawa al’umma da kawo ci gaban kasa.

Shawarwari

Shawata ta farko ita ce, ga abokan huldarmu wato dalibai, shawarar da zan ba dalibai a nan ita ce su dage wajen yin karatu, tare da nisantar dukkan abin da ka iya kawo musu cikas wajen samun nasarar a kana bin da suka sa a gaba.

Baya ga wannan yakamata dalibai su fahimci cewa, ilimi na tafiya ne tare da tarbiyya, saboda haka duk inda aka bar daya daga cikinsu, dole a samu matsala. Wannan ta sa duk dalibin da ke bukatar samun nasarar rayuwa dole ya hada koyon karatu da tarbiyya.

Ga sauaran al’umma kuma ina kira gare su da su rike gaskiya da adalci, domin ta hanyar rike gaskiya ne kadai mutum zai samu nasara a rayuwar ta duniya da kuma yin kyakkyawan karshe. Yin adalci kuwa shi ne ginshikin zaman lafiya a cikin al’umma, saboda haka idan al’umma suka zama masu adaci za a samu tabbatar zaman lafiya a kasa. Arziki zai yalwata ra kuma za ta habaka.

Haka kuma ina kira da babbar murya musamman ga al’ummar da ke Arewacin kasar nan da su kara kaimi wajen ilimantar da ‘ya’yansu, domin shi ilimi shi ne kinshikin ci gaban rayuwa, shi ke fitar da al’umma daga cikin kangin talauci, shi ne kuma ke wayar da kan al’umma yadda za su fahimci rayuwar duniya da kuma samun rahamar Allah a rana-gobe. Saboda haka ya zama wajibi mu taimakawa’ya’yanmu na jinni da makusantanmu da ma sauran al’umma baki daya wajen koya musu ilimin addini da na zamani.    

Ga gwamnati kuwa zan tunatar da su ne kan nauyin da yadoru a kansu na kiyaye rayuka da dukiyoyi da kuma tabbara da adalci a tsakanin al’umma. Daga cikin irin wannan nauyin akwai bai wa ‘yan kasa ingantaccen ilimi wanda da shi ne za samu habakar tattalin arzikin kasa da ci gaban rayuwar al’umma.

Haka kuma ya zama wajibi ga gwamnati ta tallafawa dukkan sauran bangarori kamar na noma da kasuwanci  wajen ganin an samu ci gaba mai dorewa. Kuma ida gwamnati za ta bayar da wannan tallafi ta tabbatar da cewa, ta damka amanar raba tallafi ga mutane nagari, ba wadanda za su bayar inda bai cancanta ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!