Connect with us

RAHOTANNI

Fulani Ne Koma Baya Wajen Cin Moriyar Gwamnati, In Ji Shugabar Mata Fulani

Published

on

Shugabar matan Fulani ta Nijeriya, karkashin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah da Kautal Hore, Hajiya Baheejah Mahmood Abdullahi ta bayyana cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi gami da kananan hukumomi sun mance da al’ummar Fulani makiyaya ta fuskacin samar musu da kayayyakin more rayuwarsu da na dabbobinsu.

Hajiya Baheejah Mahmud ta yi wadannan kalamai ne lokacin da take zantawa da manema labarai a Bauchi, ta ce Fulani su ne kawai kabilar da a yau ba su cin moriyar kayayyakin more rayuwa na gwamnati kamar lantarki, ruwan sha, asibitoci, hanyoyi, ilimi da kayayyakin kawa duk da irin gudummawar da suke bayarwa wajen gina tattalin arzikin kasar Nijeriya.

Baheejah ta ce rayuwar Fulani makiyaya a kullum na kara shiga cikin wani irin mawuyacin hali saboda tsana na ba gaira ba sabab.

Ta ce Fulani ba masu aikata miyagun laifuffuka ba ne, “duk Bafulatanin kirki za ka same shi mutum ne mai gaskiya haziki mai aiki tukuru wanda ba yi da lalaci mai bin dokar kasa yana biyan haraji da jangali yana kuma bada gagarumar gudummawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da nama da Madara da koyi da kuma fatu,”

Shugabar matan ta kara da cewa, “ku lura yau a duk duniya da wuya ka samu kabilar da bata aikata wani laifi, a kulum Jami’an tsaro  na kama masu laifin amma kun taba jin in an kama masu laifin ana fadin cewa dan kabila kaza da kaza ne ya aikata wannan laifin? Me ya sa sai na Fulani ake ambata wa? wannan tsanace a fili karara,” A fadinta.

Ta ci gaba da cewa “Yakamata in an kama masu laifi a bi diddigi a ga ta ina ne suka aikata laifin kuma su wanene suka sanyasu aikata wannan laifin me ya sa su aikata wannan laifi, in an yi haka sai ka ga an samu bakin zaren kuma an yi musu adalci,” A cewar ta.

Shugabar matan ta ce; “Fulani sun fi samun kayayyakin kyautata rayuwa a duk fadin Nijeriya lokacin mulkin mallaka fiye da wannan zamani don a lokacin turawa Malaman Jami’a sun shaida mana cewa Turawa suna yiwa Fulani burtalin Shanu, suna gina musu madatsun ruwa suna kuma samar musu da dajin kiwo da audugar shanu ana kuma yi musu huji da allurar riga-kafi, amma a yau duk wadannan babu, na karanta an ce yau a Nijeriya akwai burtalin shanu da dazuzzukan kiwo kowanne sama da 600 a arewacin Nijeriya da gyarasu kawai gwamnati za ta yi, me ya sa gwamnatin ba za ta yi ba ko Fulanin ba sa cikin wadanda suka zabeta ko su ba ‘yan Nijeriya ba ne?”

Hajiya Baheejah ta kuma ce abin kunya da takaici ne gwamnatin tarayya ta gaza samar wa Fulani da rugage domin kiwo, amma gwamnatin ta iya ware kaso masu tsoka da ya kai Dalar Amurka biliyan ($3.9) don gina tashar Jiragen Ruwa, sannnan ta kuma ware dala miliyan ($99.6) wanda ya kai Naira biliyan (N35.8 billion) don gina tashar sauke kaya kantudu a garin Ibadan.

Ta jawo hankalin gwamnatoci domin su dawo da batun shirin samar da rugage don kwalliya ta biya kudin salubo, a cewarta samar da rugagen zai taimaka matuka wajen yin adalci a tsakani.

Daga bisani ta fadi cewar kabilu da daman gaske sun fi su cin gajiyar gwamnatoci don haka ne ta nemi a samu sauyi kan hakan domin ci gaban kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: