Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Kaduna Na Ci Gaba Da Yin Rusau

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna har yanzu tana ci gaba da gudanar da rushe shagunan da aka kafa su ba a bisa ka’ida ba a wasu sasasan jihar ta Kaduna.

Tunda dai farko lokacin da Gwamnatin jihar Malam Nasir El-rufa’I ya dare karagar mulkin jihar a shekarar 2015 ya kikiro da shirin rusau don raya birnin jihar.

Gwamnatin ta  sanar da cewa, a wannan karo, za a rusa gidaje akalla 100 domin fadada hanyar mota

Ta kuma yi yi barazanar cewa, ba za za ta bada wani tallafi ga wadanda za a rusawa gine-ginensu.

Gwamnatin ta na gudanar da rusau ndin ne ta hanyar hukumar raya birnin jihar Kaduna KASUPDA kuma hukumar ce ta kaddamar da atisayen rusau din a fadin jihar.

A cewar Diraktan bincike na hukumar, Omega Jacob ne ya sanar da hakan ga yan jarida a jihar.

Omega Jacob ya ci gaba da cewa, ana gudanar da rushe-rushen ne saboda gine-ginen zamani a jihar domin cigaban tattalin arzikin jihar.

Ya yi nuni da cewa, hakan zai kuma bayar da dama don a fadada hanyoyin mota daga Waff road zuwa shataletalen NEPA dake a kan titin na WAFF, zuwa titin makarantar kudi ta  Essence dake a kan titin WAFF da zuwa titin Alkali da kuma titin Isa Kaita.

A cewarsa, aikin zai shafi masu shagunan dake hanyar da tuni aka aika masu da sako gudanar da aikin.

A karshe Jcob ya ce, babu wata diyya da za a biya wadanda abin ya shafa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: