Connect with us

RAHOTANNI

Hukumar Shige Da Fice Ta Bayyana Samun Gagarumar Nasara Wajen Yi Wa Baki Rajista

Published

on

A ranar Juma’ar nan hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), ta gudanar da taron manema labarai domin bayyana irin nasarori da hukumar take samu wajen yi wa baki rajista.

Taron ya gudana ne a shalkwatar hukumar da ke garin Abuja.

Da yake yi wa manema labarai bayanin irin nasarorin da hukumar ta samu, shugaban hukumar NIS, Muhammad Babandede ya bayyana cewa, hakki ne da ya rataya a kan hukumar NIS ta yi wa baki ‘yan kasar waje rajista kamar yadda shugaban kasa ya bayar da umurni.

“Kamar yadda na yi bayani a jiya, hakkin hukumar ne ta yi wa baki ‘yan kasar waje rajista. Doka ta bayyana cewa, duk wanda zai zauna a Nijeriya fiye da kwana 90, to dole sai an yi masa rajista, idan kuma ya ki yin rajista, to ya aikata laifi. Domin bai wa bakin damar yin rajista, shugaban kasa ya yi musu afuwa na tsawon wata shida domin su je su yi. Wannan afuwa na rajistan baki zai kare ne a watan Janairun shekarar 2020. Ana yi wa bakin rajistar koda ba su da wata takarda, amma daga baya  kan shawarce su da su sami fasto daga ofishin jakadancinsu. Dokar ta bayyana cewa, idan bako ya zo yin rajistar, ana daukarsa ne a matsayin wanda ya shigo Nijeriya a wannan lokaci.

“Yin rajistar ba yana nufin cewa, bakin sun zama ‘Yan Nijeriya ba ne, zama dan kasa ya ta’allaka ne ga tsarin mulkin kasa. Afuwan da shugaban kasa ya bayar ba tana nufin an bai wa bakin damar yin laifuka ba ne, ba kuma yana nufin su zauna a kasar ba tare da ka’ida ba. Lokacin da shugaban kasa ya kaddamar da cibiyar a Abuja, hukumar ta yi kokarin bude cibiyoyin aikin a dukkan jihohin kasar nan” in ji shi.

Shugaban na NIS, Babandede ya ci gaba da cewa, zuwa yanzu hukumar ta yi wa baki rajista masu yawan gaske. “Akalla hukumar ta yi wa baki 2,175 rajista a garin Abuja kawai. Ma fi yawa daga cikin wadnda aka yi wa rajistar suna zaune ne a cikin kasar nan ba bisa ka’ida ba,” a ta bakinsa.

Jami’an Hukumar NIS suna wa baki rajista a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

 

Har ila yau, Babandede ya ce hukumar ta yi wa baki sama da 4,373 rajista kasar bakidaya. A cewarsa, bayan wa’adin da aka bai wa bakin su yi rajista ya kare, za a fitar da duk wani bakono da bai yi ba daga cikin kasar nan aka samu bai yi rajista.

Shugaban na NIS, ya shawarci bakin da su yi amfani da wannan dama su tabbatar da sun yi rajista kafin lokacin da shugaban kasa ya ba su ya shude.

Wasu bakin kasashen waje da suka je shalkwatar Hukumar NIS domin yin rajista.

 

Shi ma babban jami’in kula da cibiyar yi wa baki rajista a shalkwatar hukumar, Aliyu Ahmad Bauchi, ya bayyana irin nasarori da cibiyar ta samu wajen yi wa bakin rajista.

Ya bayyana cewa, tun daga lokacin da cibiyar ta fara yi wa baki rajista a ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2019, bakin ‘yan kasar waje sun amsa kiran hukumar, inda suke ta zuwa ana yi musu rajista.

Ya ci gaba da cewa, bakin da dama sun samu yin wannan rajista, sannan wasu kuma suna kokarin zuwa domin a yi musu.

Aliyu ya ce, hukumar NIS tana samun nasarar gudanar da aikin rajistar a cibiyoyinta daban-daban na kasar nan.

Taron ya samu halattar manema labarai masu yawan gaske, inda manema labaran suka tattauna da wasu bakin da suka yi rajista a hukumar. Inda suka bayyana cewa, sun kwashe sama da shekaru 10 suna zaune a cikin Nijeriya ba tare da wani izini ba.                  
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!