Connect with us

LABARAI

Kwana 100 A Ofis: Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Muhimman Ayyukan Gwamnatinsa Guda Hudu

Published

on

A wannan makon ne gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya cika kwanaki 100 a ofis; matsayin zababben gwamanan jihar, wanda a daidai lokacin ne ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaban jihar wadanda suka kunshi aza harsashen ginin babbar tashar manyan motocin dakon kaya a garin Potiskum tare da sake farfado da kamfanonin fulawa da na kwanon rufi (Flour and Feed Mills and Sahel Alminium) duk a garin Potiskum.

Sauran ayyukan su ne dora harsashen ginin sabbin gidaje 3600 kana da sabbin motocin noma da takin zamani ga manoman jihar a farashi mai rahusa. Wadannan muhimman ayyuka ne wadanda za su farfado da jin dadi da walwalar jama’ar jihar wadda ta sha fama da matsalolin tsaro; kimanin shekaru tara da suka gabata.

A jawabin Gwamna Mai Mala Buni a bikin kaddamar da tashar manyan motocin dakon kaya da sake dawo da ayyukan wadannan kamfanin, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne don samar da aikin yi ga matasa, fadada hanyoyin kudin shiga tare da bunkasa harkokin tattalin arzikin yankin da ma jihar baki daya.

Mai Mala Buni ya ce aikin gina tashar manyan motocin ya na daga cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe- wadda gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Nijeriya ( National Shipper’ Council) wadda ya ce ita kadai za ta iya samar da guraben ayyuka 5,000 ga yan jihar.

Ya kara da cewa, babbar tashar manyan motocin dakon kaya- mai fadin murabba’in kadada 50 (hectares) za ta kunshi isassun ruwan sha, hanyoyi da dakin shan magani- don kula da jin dadin direbobi da kula da lafiyar su.

A hannu guda kuma, ya shaidar da cewa gwamnatin ta cire naira miliyan 174.44 domin ganin kammala aikin farfado da kamfanonin. Mudaden da za a yi amfani dasu wajen sayo kayayyakin da kamfanonin ke bukata don ci gaba da gudanar da aikin.

Haka kuma, ya yi kira ga ma’aikatar masana’antu ta gwamnatin tarayya, hukumar bunkasa harkokin kasuwanci da zuba hannun jari tare da na yan kasuwa masu zaman kan su da cewa su zo su giggina masana’antu da kamfanoni a jihar Yobe.

A gefe guda kuma, Mai Mala Buni ya jagoranci dora harsashen ginin sabbin gidaje 3,600 wadanda za a samar a fadin jihar. Inda a jawabin Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta gina wadannan gidjen ta hadin gwiwa da ma’aikatar kudi ta tarayya tare da kamfanin Family Homes Ltd, kuma a farashi mai rahusa ga masu karamin karfi.

Ya ce “Burin kowane mutum ace ya sururce kan sa; ma’ana ya mallaki muhalli na kan sa. Wanda wannan shi ne babban dalilin da ya sa gwamnatin jihar Yobe ta tashi hakkan wajen ganin ta samar da yanayin da kowa ya samu gidan kan sa kuma lilwantacce da inganci”.

“Kuma yau gashi mun kaddamar da gina wadannan gidjen, amma ina son ku fahimci cewa biyan diyyar filayen da wannan aikin ya shafa, yana bisa wuyan kamfanin Family Homes Funds limited. Wanda yanzu haka kananan hukumomi suka aikin tantance kimar filin kowane mutum”. 

A bangaren ayyukan noma kuma, a lokacin da Mai Mala Buni ke cika kwanaki 100 a ofis, ya kaddamar da sayar da takin zamani ga manoman jihar tare da motocin noma 103 don raba wa ga kananan hukumomin jihar 17. 

Ya ce halin da jihar Yobe ta shiga na matsalar tsaro ya jawo jama’an tsaro sanya tarnakin hana shigo da takin zamani a jihar bisa kan kari, wanda dakyar gwamnati ta samu izinin shigo da shi. Inda ya kara da cewa ya bayar da umurnin a sayar wa manoman da buhun takin NPK  kan farashi naira 3, 000.00.

Kana ya ja kunnen jama’ar jihar kan cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunta da fita wata jihar da wadannan motocin ba balle kuma fasa-kwaurin takin zuwa wasu jihohin kasar nan ba.

Da yake tofa albarkacin bakin sa, sakataren din-din-din a ma’aikatar ayyukan gona da albarkarun kasa, Alhaji Mangarima Lawan, ya bayyana cewa, cikin kasa ga kwanaki 100, gwamnatin jihar Yobe ta zuba sama da naira biliyan uku  (3) a harkokin noma a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!