Connect with us

MANYAN LABARAI

Nijeriya Ba Za Yanke Huldar Jakadanci Da Afirka Ta Kudu Ba – Gwamnatin Tarayya

Published

on

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa Nijeriya ba za yanke huldar jakadanci da Afirka ta Kudu ba, sakamakon nuna tsanar da aka yi wa ‘yan Nijeriya a kasar.

Onyeama, ya fadi haka ne a jiya Juma’a lokacin da ya bayyana kwamitin da majalisar Dattijai ta kafa kan nuna tsanar da aka yi wa ‘yan Nijeriya a kasar ta Afirka ta Kudu.

Ya ce, kididdiga ta nuna cewa, akwai ‘yan Nijeriya sama da 800,000 da ke da izinin zama a kasar, saboda haka matukar Nijeriya ta yanke huldar jakadanci tsakaninta da kasar ta Afirka ta Kudu zai shafi rayuwar wadannan ‘yan Nijeriya ta fuskar rayuwarsu ta yau da kullum da kuma harkokin kasuwancinsu.

Ya ce, shugaban kasa Muhammadu ya tura tawaga ta musamman wadda za ta je babban birnin kasar, kuma a yau Asabar ne ake sa ran za su dawo da bayani.

Ya ce, rahoton da suka zo da shi, za a yi amfani wajen daukar matakin da ya dace. Ya kara da cewa, ba sa tunanin yanke huldar jakadanci domin kuwa akwai hanyoyi da dama wadanda za a iya bi domin warware wannan matsala.

“Lokacin da wannan rikici ya balle, Hukumar jirgin sama ta Nijeriya ta kai jirgi domin kwaso ‘yan Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: