Connect with us

LABARAI

NNPC Ya Yi Barazanar Korar Ma’aikata 1,050

Published

on

Kamfanin NNPC ya yi shelar cewa, zai kori ma’aikatan sa guda dubu 1,050  saboda aikata rashin gaskiya da cin amana da kuma cin hanci da rashawa.

Babban Manajin Daiarktan rukunonin kamfanin na  NNPC, Mele Kyari ne ya sanar da hakan, inda ya kara da cewa, ma’aikatan Depot suka shahara wajen yin badakala sune abin zaifi shafa.

Mele Kyari ya kuma shedawa manajojin ma’ajiyar da ma’aikatan cewa duk wanda aka kama da rashawa zai rasa aikinsa ba tare da wani bata lokaci ba.

Babban Manajin Darktan rukunonin kamfanin ya sanar da hakan ne a jawabin sa  a lokacin taron cin abincin dare da aka shiryawa ma’aikatan kamfanin na NNPC.

Mele Kyari  ya shawarci ma’aikatan kamfanin na NNPC  akoda yasuhe su kasance masu yin gaskiya a yayain da suke gudanar da ayyukansu don kamfanin ya cimma burin day a sanya a gaba.

A cewar Babban Manajin Daiarktan rukunonin kamfanin na  NNPC, Mele Kyari ba zai lamunci cuwa-cuwan da aka saba yi a baya ba, duk ma’aikacin da aka kama da rashawa zai fita da ma’akatara ba tare da bata lokaci ba.

Babban Manajin Daiarktan rukunonin kamfanin na  NNPC, Mele Kyari ya kuma  ja hankalinsu kada su kutsa kawaunan su a cikin dukkan abinda suka sanya badakala ce.

A karshe Babban Manajin Daiarktan rukunonin kamfanin na  NNPC, Mele Kyari ya ce hukumar za ta karrama duk ma’aikacin da ya gudanar da aikinsa da kyau.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: