Connect with us

MANYAN LABARAI

Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe Ya Rasu

Published

on

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya kwanta dama. Ya rasu yana da shekara 95. Sanarwar rasuwar ta sa ta fito ne ta bakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ta kafar sadarwar Twitter wanda ya ce, marigayi Mugabe ya rasu a wani asibiti da ke kasar, haka kuma wata majiya mai tushe ta shaidawa kamfanin Dillancin labarai na Reuters wannan labari.

“Cikin alhini ina sanar muku da rasuwar tsohon dan gwagwarmaya kuma tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Cde Robert Mugabe,”.

A cikin watan Nuwamba ne, Mnangagwa ya bayyana cewa, rashin lafiyar Mugabe ta yi tsanani, har ta kai ga baya iya tafiya, wanda a wannan lokacin ne aka kai shi wani asibiti da ke kasar Singapore.

Wata majiya ta bayyana cewa,

an yi wa marigayin aikin ido ne, wanda kuma wannan bayanin ya karyata wata jita-jita da ake yi na cewa, an yi masa aikin cutar kansa ne.

Mugabe, ya shugabanci ‘yan kasar Afirka ta Kudu na kusan tsawon shekara arba’in, tun daga lokacin da suka samu ‘yancin kai a shekara ta 1980, sai a cikin watan Nuwamba na shekara ta 2017 aka matsa masa ya yi murabus bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Ya kai ga matsayin faitaccen dan gwagwarmaya kuma jagoran yaki wariyar launin fata.

A wata sanarwa da  mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman a fannin yada labarai Femi Adesina, ya fitar, ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu buhari ya nuna alhininsa bisa wannan rashi da al’ummar Afirka suka yi inda ya ce “A madadin gwamnatin tarayya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin da kuma dukkan al’ummar Zimbabwe bisa wannan babban rashi da aka yi na dan kishin kasa kuma tsohon shugaba, Robert Mugabe wanda ya rasu yana da shekara, 95.

“Haka kuma shugaban kasar ya yi wa iyali da kuma dukkan abokan gwagwarmayar marigayin ta’aziyya wanda ya tsaya tsayin daka wajen ganin kasar tasa ta samu ‘yancin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka.

“Shugaba Buhari ya nuna irin sadaukarwar Mugabe ya yi a alokacin rayuwarsa wajen bunkasa harkokin siyasa da tattalin arzikin kasar. “Saboda haka sai ya roki Allah ya gafarta masa kura-kurensa.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!