Connect with us

RAHOTANNI

An Koka Kan Rashin Yin Ingantattun Hausa A Gidajen Radiyo

Published

on

Kungiyar kwararru a kan harkar tallace-tallace ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana damuwarta kan yanda ake samun gurbacewar harshe a cikin tallace-tallacen da ake a kafafen yada labarai.

Shugaban kungiyar Kwamared Sammani Sharif ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da wani gidan rediyo a Kano da aka tattauna dashi akan magance matsalar gurbatar Hausa a cikin tallace-tallace.

Ya ce, koma bayane ga harshen Hausa ta yanda ake bai wa wadanda ba harshensu suyi talla sannan a sanya a yankunan da ake harshen Hausa.

Ya ce, yawanci tallace-tallace da ake sanyawa a gidajen radiyo da allon tallace-tallace akan tituna Hausace mara dadi kamarma babu masu jin harshen Hausa.

Yakamata su hada kansu waje daya ya zamanto duk wata talla da za’a kawo Arewa inda Hausa aka yishi ya zama an yi da Hausa cikakkiya sannan mutanen da suke basu da lasisi na gudanar da harkar tallace.

Kwamred Sammani Sharif ya kuma ce, kungiyarsu na kokarin wayar dakai ga jama’a ta shirya taron wayar dakan jama’a nan gaba kadan.

Dama dai jama’a da dama suna yawan kokawa da yanda ake sanya talla ba tareda cikakkiyar Hausa ba musamnan a gidajen radiyo sabbi da ake budewa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: