Connect with us

RAHOTANNI

An Sace Hafsan Soja A Kaduna

Published

on

An bayar da rahoton sace wani hafsan Soja mai mukain Laftana, wanda wasu ‘yan bindiga suka sace shi a wani kanti da ke Zariya, Jihar Kaduna.

Mutanan da suka ga faruwar lamarin sun shaida wa wakilinmu cewa Sojan wand aba shi a cikin tufafinsa na aiki ya tafi kantin ne da nufin sayen wasu abin bukatu na shi a lokacin da masu satan na shi suka iso wajen suka watsa mutane kowa yay i ta kansa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwan lamarin a tattaunawar waya da aka yi da shi a ranar Asabar.

An bayar da sunan jami’in Sojan da aka sace da, Laftana A Falana.

A cewar rahoton ‘yan sanda, “A ranar Litinin da yamma ne aka sace shi, amma tuni ya iya tserewa daga hannun wadanda suka sace shi din ba tare da ya sami ko kwarzane ba.

An shaida mana cewa an sace shi ne a wani kanti da ke kusa da jami’ar ABU a ranar Litinin da yamma, ann ya tsere daga hannun wadanda suka sace shi din ba tare da ya sami ko kwarzane ba. amma wata majiya ta soji wacce ba ta so a ambata sunan ta ba ta karyata faruwar lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!