Connect with us

RAHOTANNI

An Yaba Wa Gwamna Ganduje Kan Bayar Da Ilimi Kyauta A Jihar Kano

Published

on

An bayyana abinda Gwamnan Kano ya yi na bada ilimi kyauta kuma wajibi a makarantun furamare dana sakandire a jihar Kano da cewa, ya yi abinda yakamata. Malam Auwalu Sulaiman Shugaban Annur “Institute for Islamic Education” ya bayyana haka jim kadan da kaddamar da shirin a Kano

Ya yi nuni da cewa wannan shine abu mafi kyau da kowane shugaba zaiyi a tarihinsa na mulkin al’ummarsa  domin ilimi shi ne tushen kowane cigaba in babushi ba zancen samun cigaba.

Yace ilimin nan gaba daya dole a fadada a baiwa dan mai hali da dan mara hali domin su sami iliminnan gaba daya saboda haka dole su yabawa Gwamna Ganduje a bisa wannan yunkuri da ya yi na kaddamarda bada ilimi kyaura ga ya’yan jahar Kano da mazauna Kano.

Malam Auwalu Sulaiman Darma yace in akayi duba ga shugabannin yanzu mafi yawancinsu ba wanda ba Gwamnatice ta dauki nauyin karatunsa ba,basu san meye sayan unifom ba ko littattafai hatta sabulun wanka basu ake.Ire-iren wadannan da sukaci moriyar bada ilimi kyauta na Gwamnati a baya sunefa shugabanni ayau amma abin takaici mafi yawancinsu sune wanda suke dakile duk  wani yunkuri na baiwa dan talaka ilimi domin su cigaba da rike ragamar mulki a hannunsu har abada a zatonsu dan wajibine a yabawa Gwamna a bisa wannan kyakkyawar niyya.

Yace shigarda makarantun Islamiyya zaisa abin ya yi nasara domin koda a baya in aka tafi karkara za’asa yara a makaranta in babu malamin arabiyya baza’a kawo yara makarantar ba.Ilimin Islamiyya dana Arabiyya ya zama wajibi a tafi dashi domin duk wani ilimi da bazai koyarda tarbiyyar addini ba mutane na kaffa-kaffa dakai ya’yansu makarantar.Ilimin larabci dana addini a cikin makarantun furamare da sakandire abune mai kyau.

Malam Auwal Sulaiman ya kara da cewa a makarantu yanzu akwai furamare da sakandire na Islamiyya in aka dauki adadinsu aka auna da makarantun da ake dasu na Gwamnati sun rinjayesu, wannan alamace in ana son cimma gaci dole ne ayi tafiya da ilimin Islamiyya a makarantun Gwamnati.

Malam Auwal ya kafa misali da cewa a lokacin da yake aiki a ofishin kulada harkokin ilimin addinin musulunci “Islamic education centre” wanda daga baya ta zama”Islamic education bereau” Wanda yanzu aka mai dashi “Department” A ma’aikatar ilimi, a lokacin sun kula cewa in akayi jarabawar shiga makarantun sakandire.Makarantun Islamiyya da suke cin jarabawar shiga makarantun boko sun haura da kashi mai yawa na wadanda suke makarantun furamare na Gwamnati.

Yace rungumar ilimin Isamiyya ga dukkannin wata Gwamnati mai sanin yakamata kamar bada damane na kara habaka ilimi gaba daya. Zaka ga daliban makarantun Islamiyya sun yi fice  bawai a ilimin larabci kona Islamiyya ba,hatta a turanci da lisssafi sun dara yan makarantun boko zallah samun maki,saboda haka abune da aka yishi akan gaba suna fata Allah ya cigaba da karfafar  niyyar Gwamna ya azurtashi da jajirtattun wadanda zasu taimakawa wannan yunkuri nasa.

Malam Auwal Sulaiman ya yi kira ga iyaye su yiwa Gwamna Ganduje jinjina bisa wannan abu da ya yi su bada sukkan goyon baya da yakamata domin ganin ba’a sami cikas ko wani sartse ga wannan kyakkyawan tanadi na Gwamnatin Kano na bada ilimi kyauta.Iyaye su fito da gudummuwarsu komai kankantarta domin cimma manufa ta Gwamna bawai dan ance komai kyauta ba, kowa ya janye hannu,dole a taimakawa Gwamnati ta bangaren tallafawa yunkurinta inda akaga ba daidai ba a bata shawara na gyara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!