Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (59)

Published

on

Asawadu ya kalle ta ya ce, lallai yarinya yau kin hau mataki mai wahalar da ba za ki sake hawa mataki kamarsa ba, sannan kuma na tabbata a baya baki taba hawa kamarsa ba. “ Wannan ita ce makaskanciyar ranar da dadai ban taba tsammanin ganinta a rayuwata ba, amma ina so ki sani cewa, barinki cikin wannan alkarya da wannan muhimmin tarihi shi ne abu mafi girman bakin ciki a gare ni,” in ji shi.

Sarauniya Hamdiyatul’aini ta ce, “ Ai na taba kashe wanda ya fi ka girma da karfi da alamu na ban tsoro, wanna kuma ya faru tun ina kan koyon yaki, tun kafin na kai ga samun nadin sarauta, ballantana yanzu da nake mulkar babbar alkarya, zan kashe ka kuma zan kafe kanka a tsakiyar garin domin mazowa wannan alkarya su tabbata da mutuwarka gami da shafe tarihinka a ban kasa. Iyayenka sun haife ka sun bar duniya da nufin suna da magaji da za a rika tunawa da su a ban kasa, yau kuma ga shi za ka mutu ka bara duniya ba tare da ka bar da ko jika ba, za ka mutu a shafe tarihinka a ko ina cikin duniya, wannan shi ne babban kuskurenka na rshin yin aure.

“ Yanzu ina sauraron ka ko akwai sako da za ka ba wa duniya da zai amfanar da al’umma duk da na san baka taba aikata wani abin alheri a iya zaman duniyarka ba.” Aswadu ya cira kai cikin magagin mutuwa kamar zai yi magana, amma ina hankali ya fara gushewa, ba ya iya komai sai dai kallonta.

Ta duba ta ga jama’a sun fara taruwa ta ce, wa zai iya gaya min halin da sarkinku yake ciki? ko ya yi shiru, daga nan ta ce, idan ban da Allah babu wanda ya san abin da yake gamuwa da shi a halin yanzu, abin da zan iya sani a halin yanzu shi ne, na san yana cike da nadamar kasancewarsa ba Musulmi ba. haka lamarin yake ga duk ya zo mutuwa babu imani.

Ta daga takobi ta daidaici wuyansa ta sake kafta masa sara, saboda karfin saran da iyawa sai da kansa ya rabu da wuynsa fit, ta daga hannu sama ta yi kabbara sau uku jama’a suka amsa.

An jiyo sautin kiran Sallah daga wata doguwar hasumiya dake babban masallaci dake tsakiyar garin, an jiyo carar wani gwado-gwadon zakara daya daina carat un bayan da Aswadu ya fara mulki. Wasu nau’in tsuntsaye masu kama da jemagu sun yi ta fitowa daga cikin babban azure daga cikin zaurukan fadar gidan. An jiyo shewar wani dila gami da kukan dawisu wadanda ba’a ji sun yi ba, an ga wadansu jariran zakuna masu dauke da fatar buzun kura a bayansu suna ta fitowa, da sauran abubuwa na ban aljabi.

Hamdiyatul’aini ta ce, ku yi duba izuwa ga abin da sarkinku yake aikatawa a cikin gidan sarauta, wadannan abubuwa da kuke gani duk ba komai ba ne illa al’amura na sihiri, wanda dukkansu a yau Allah ya kawo karshensu . “ Zan shiga cikin gidan idan akwa wanda yake da kwarin zuciya ya biyo domin kammala aikin da muka fara.”

Ta shiga cikin gidan takobinta a zare duk wani abu da ta yi arba da shi in har bata aminta da shi sunansa gawa, ta doshi wani bakin daki mai girma da fadi wanda ta ga hayaki na fita daga cikinsa kadan-kadan, sai ta ji an ce idan kika shigo sai mun hallaki.

Ta zare kibiya ta sanya a baka ta harba ciki, sai ta ji wata irin kara mai ban firgici, kasar wurin ta dauki zalzala, sai ga wata dabba mai kama da gwanki ya fito daga ciki yana fitar da wani irin hayaki daga bakinsa mai zafi, gidan ya dauki hayaniya ta sautin abubuwa iri-iri, ya fito yana ta dube –dube kai ka ce shi mahaukaci ne, ta sake harba masa guda daya nan take ya fadi yana ci da wuta, tun daga nan ta ji gidan shiru kamar ba a taba yin wata hayaniya ba, daga baya ta ga dakin ya washe kamar ba’a taba yin wani na sihiri a ciki ba.

Bayan ta kammala da da duk abin da yake gidan, sai ta fito waje ta yi umarni da a samu wasu mazaje su fito da duk kan kayan cikin gidan a kone su. Ta zauna a wannan alkarya muddar kwana uku aka tabbatar da babu wani na wancan shakiyyin sarkin, sannan ta sa manyan garin da Malaman garin suka zabi Sarki, aka nada babban dan sarkin da Asawadu Dan Sauda’u ya kashe, mai shekaru talatin da biyar bisa sarautara Kasar.

Bayan da aka kammala daidaita al’amura, Hamdiyatul’aini ta ce, za ta koma can Manzila, jama’ar gari fa suka ce ai basu san haka ba, gara dai ta zauna zuwa kamar shekara guda sannan sun tabbatar komai ya koma yadda yake.

Hamdiyatul’aini ta basu hakuri, sannan ta fada “ Ai na ba Kasa ta ba ce, kuma abin da na zo yin a nan na yi kuma na kammala, don haka ya zama wajibi a yi hakuri na koma inda na fito.” A nan ne ta mince ta za ta cika mako guda sannan ta koma Ksarta.

A dare na karshe daga dararen  kwanakinta ne sai Jassasa ta zo mata, suka gaisa ta yi mata godiya, Hamdiyatul’aini ta karbe ta hannu bibiyu. “ Jassasa ina kika shiga har kammala aiki ban ganki ba?” in ji Hamdiyatul’aini.

Jassasa ta ce, “ Allah ya ba ki nasara al’amarinki ya girma, ai ranar da zaki afka wa lambun boka na so a ce da ni a ka yi komai, na zo daidai Anharussalasa na ga an girke wata rundunar aljanun Musulmai dauke da manyan makamai kamar dai za su kai hari ne wata alkaryar aljanu, da na ga haka sai koma da baya, domin na san jama’aku ne suke jira idan lamari ya yayi tsanani gareki su kawo miki dauki. Hamdiyatul’aini ta ce, Ai nasara ta zo daga Allah yanzu an yi nadin sabon sarki, kuma idan Allah ya kai mu gobe zan koma Manzilatussurayya don ci gaba da abin da muka saba.

Bayan sun yi sallama da Jassasa ta kwanta bacci sai ta yi wani mafarki da ta ya tayar mata da hankali, ta tashi a dugunzume ga shi kuma babu wani daga cikin masu bata shawara a kusa. Kashe gari ta shirya cikin gaggawa ta koma Manzilatussurayya domin neman shawara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!