Connect with us

TATTAUNAWA

Da Sana’ar Gyara Takalmi Na Sayi Gida –Adamu Shoe Shiner

Published

on

Wakilinmu Muhammad Sani Samaru ya tattauna da Malam Adamu Ibrahim wanda yake sana’ar gyaran takalmi a kan layin Adamu Hadejia dake Hayin Dogo Samaru Zariya ta jihar Kaduna, inda ya bayyana masa wasu  daga cikin sirrorin dake tattare da sana’ar da kuma irin amfanin daya samu a cikin sana’ar a shekaru goma sha biyar da ya yi yana gudanar da sana’ar, ga dai yadda hirar tasu ta kasance.

Da farko zamu so ka fada mana sunanka?

Sunana Adamu Ibrahim amma anfi sanina da  ‘’Ado shoe shiner’’

Mene sana’ar ka?

Sana’ata  itace gyaran takalmi da poolish

To, Malam Wannan Sana’a Gado Ka Yi Ko Koya Ka Yi Daga Wani?

A gaskiya ni ban gaji wannan sana’a ba amma cikin ikon Allah mahaifina ya kaini wajen wani abokinsa na koyi wannan sana’a, a halin yanzu na yi fiye da shekara goma sha biyar ina cin gashin kaina.

Wani Anfani Ka Samu Ta Hanyar Wannan Sana’a?

Gaskiya Alhamdulillahi babu abin da zamu ce sai dai mu gode ma Allah saboda mun samu rufin asiri sosai ta hanyar wannan sana’a. Da wannan sana’ar ta gyaran takalmi na sayi gidan da nake zaune a ciki da iyalina kuma dashi nayi aure yanzu haka ina da yara biyar. Da wannan sana’a nake biya masu kudin makaranta kuma dashi nake biyan kudin hayan shagon da nake ciki har kuma nake iya taimaka wa mabukata  a cikin dangi da al’ummnar Annabi, Alhamdullilahi.

Da Yake Kaima Wani Ne Ya Koya Maka Wannan Sana’ar To A Yanzu Mutum Nawa Ka Koya Wa Sana’ar Kaima?

To Allah cikin ikonsa na koya wa mutane akalla mutum uku wanda suma yanzu suna can sun bude shago suna cin gashin kansu duk da haka kuma akwai wasu yara biyu da suke ci gaba da koyan wannan sana’a akarkashina a halin yanzu, suna kuma zuwa makarantar boko don samun ilimin zamani, in sun taso makarantar ne suke zuwa koyon akin da lokauttan hutu.

Wani Jari Mutum Yake  Bukata Domin Fara Wannan Sana’a ta gyaran takalmi?

Wannan sana’a tamu bata bukatan wani jari mai yawa sosai saboda koda naira dubu uku zuwa naira dubu biyar zaka iya fara wannan sana’a kuma daidai gwargwado zaka iya samun riba sosai indai ka maida hankali a sanaar. Don zaka ga wasu suna jin kunyar yin sana’a musamman wannan sana’ar ta gyaran takalmi wato ‘’shoe shiner’’. Sai kuma kudin kama shago, wanda hakan ya danganta da wuri da kuma irin stadar kudin haya a inda mutum yake nufin kama shagon, amma lallai wannan sana’r bata bukatar wasu kudade masu dimbin yawa.

Wadanne Kalubale Ka Fuskanta A Lokacin Da Kake Koyan Sana’ar Da Kuma Lokacin Da Ka Fara Cin Gashin Kanka?

Lallai na fuskanci gaggarumin kalubale a shekarun farko dana fara koyan wannan sana’ar don kuwa wasu abokai na suna zolaya na suna mani dariyar wai don ina gyaran takalmi, har an samu lokacin dana nemi barin koyan aikin in koma wani harkar amma da yake Allah ya sa abinci na yana a sanar’ ne na daure, haka kuma na fuskancin kalubale sosai musamman ta bangaren masu bamu hayan shago saboda zaka ga wani sai ka saba da wuri kafin zai zo ya tasheka haka muke samun matsala dasu kuma zaka ga wasu mutane suna daukanmu kamar bamu da anfani saboda kawai muna sana’ar ‘shoe shiner’ a gaskiya bama jin dadin hakan kuma akwai matsalar rashin isassun kayan aiki na zamani da kuma rashi da tsayyan farashin kayan gyara a kasuwa wadannan sune daka cikin manyan kalubalen da muke fuskanta. Haka yan bashi na kawo mana cikas, sai kaga mutum ya kawo gyara bayan an kammala sai yace babu kudi.

Wani Shawara Kake Dashi Ga Gwamnati Da Masu Hannu Da Shuni A Cikin Al’umma?

Shawara ta ga gwamnati shi ne su dinga gina shaguna a kasuwanni suna bada haya ga masu sana’a don sauwaka kudaden da ake na haya kuma samar da bashi mai saukin ruwa wanda zai inganta wannan sana’a tamu don kuwa hakan zai taimaka mana samun kayan aiki na zamani ta yadda zamu samar da takalmar da zasu iya gogayya a kasuwanin duniya. Ina kuma kira ga gwamnati da ‘yan siyasa dasu daina bada matasa kudi maula a lokuttan harkar siyasa maimakon haka su dinga daukar nauyin matasan zuwa koya sana’o’i saboda idan kaba mutum kudi zai kashe amma idan ka koya wa mutum sana’a zai cigaba da samun kudi da wannan sana’a har ma ya taimaka wa wasu a nan gaba.

Idan Kuma Muka Koma Ga Matasa Wani Shawara Kake Dashi Garesu Da Kuma Iyaye Baki Daya?

Da farko zan fara ne da kira ga iyaye dasu tabbatar da yaransu sun samu sana’ar da suka dogara da ita ba wai a fuskanci karatun boko kawai ba, in har yaro yana da sana’a to zai samu abin dogaro a rayuwarsa, saboda haka ina bada shawarar a lokuttan hutun boko a tabbatar da yara na zuwa koyan sana’a, ga matasa kuma ina kira garesu da kada su raina sana’a don baka san sana’ar da zai ceceka ba a rayuwarka a nan gaba.

Malam Adamu Mun Gode Kwarai Da Gaske

Nima na gode, Allah Ya daukaki gidan wannnan jaridar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!