Connect with us

RAHOTANNI

Ganduje Ya Jajanta Wa Sarkin Suleja Sakamakon Fashewar Tankar Mai

Published

on

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jajanta wa Sarkin Zazzau Suleja, Malam Muhammad Auwal Ibrahim, bisa mummunan hadarin da ya afku a mahadar Garin Dikku kwanaki uku da suka gabata.

Hadarin  dai ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku, inda wasu mutane akalla su takwas suka gamu da munanan raunka, sannan motoci guda 19 suka kone nan take kurmus tare da shaguna kusan guda 30, wadanda wutar ta yi wa lahani.

“Ko shakka babu, wannan wani iftila’i ne daga Allah (SWT), sannan ina mika sakon ta’aziyya ta  Gwamantin Jihar Kano da sauran al’ummarta baki daya tare da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa wadanda suka mutu a lokacin afkuwar wannan hadari, Allah kuma Ya sa Aljanna ta zama ita ce makomarsu, ameen”, in ji Ganduje.

Haka zalika, Gwamnan ya yi addu’a tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka a yayin wannan hadari. Sannan ya sake yin addu’a da cewa, Allah (SWT) Ya mayar wa wadanda suka yi asarar dimbin dukiyoyinsu da kyakkyawan sakamako.

A yayin ci-gaba da jajanata wa Mai Martaba Sarkin, Gwamna Ganduje ya tuna yadda Sarkin ya

bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban Babban Birnin Tarayya Abuja, tsawon shekaru masu yawa a baya.

“Ina iya tunawa da wasu muhimman gudunmawa da ka bayar ga ci-gaban Birinin Tarayya Abuja, babu shakka ka yi kyakkyawan aiki a wannan bangare, sannan ina sake jaddada cewa, ina kyakkyawar alaka da wannan Masarauta ta Suleja, tun sama da shekarau talatin da suka wuce. Saboda haka, a duk yayin da na zo Suleja, kamar gidana na zo” in ji shi.

Har ila yau, a cewar Gwamnan, dangantaka tsakanin Jihar Kano da kuma Masarautar Suleja, ba karamar dadaddiyar  alaka ba ce, har yanzu nakan tuna lokacin da Sarkin Suleja, Mai Martaba Malam Muhammad  Auwal Ibrahim, ke koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano, a lokacin tana matsayin Kwalejin Abdullahi Bayero.

Da yake gabatar da nasa jawabin, Sarkin na Suleja, gode wa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi, bisa wannan ziyara ta zumunci, wanda a cewar tasa wannan ziyara ita kanta wata alama ce da ke kara tabbatar da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Jihar Kano da wannan Masarautar ta Suleja.

Haka nan, Sarkin ya bayyana wannan hadari da cewa, abu ne wanda ya jijjiga su tare da tayar musu da hankali kwarai da gaske. “Babu shakka, wannan hadari ya yi muni yadda ba a zato, sannan kuma lallai abin a tausaya ne. Kazalika, Gwamna Jihar Niger, shi ma ya zo wannan

Fada domin jajanta mana wannan al’amarin”, in ji Sarkin.

Har wa yau, “ni ma ina fatan zuwa Kano, domin kara dankon zumuntar da ke tsakanin wannan Masarauta da kuma Jihar Kano, domin kuwa abin da ke tsakaninmu ‘yan’uwantaka ne da kuma kyakkyawar zamantakewa”, a cewar Mai Martaba Sarkin.

Haka nan, Sarkin ya sake bayyana wa Gwamna Ganduje cewa, yana son zuwa Jihar Kano ne, domin gane wa idanuwansa irin gagarumin ci-gaban da aka samar, ake kuma kan samar wa a  Jihar, “kamar yadda muke samun bayanan irin ayyukan ci-gaban da kake aiwatar a Jihar ta Kano.”

Wani abin ban sha’awa a daidai lokacin da Gwamna Ganduje ya mike domin gabatar

da nasa jawabin a Fadar Sarkin shi ne, nan da nan Sarkin ya bukaci Gwamnan da ya zauna don gabatar da jawabin nasa a zaune.

Amma kuma, yayin da Sarkin ya fahimci cewa, Gwamna ya fi muradin gabatar da jawabin a tsaye, musamman don nuna girmamawa ga Sarkin, sai Mai Martaba Sarkin ya fada a fili kowa na jin sa cewa, “idan ba ka zauna ka gabatar da jawabin naka a zaune ba, ni ma zan mike tsaye .”

Jin hakan da Gwamnan ya yi ne, yasa ya hakura ya zauna, ya kuma ya ci-gaba da gabatar jawabinsa ga Mai Martaba Sarkin da kuma sauran Fadawansa, wannan ne yasa fuskar kowa

da ke cikin wannan Fada ta kasance cike da farin ciki da annashawa, sakamakon wannan girmamawa da Gwamnan ya samu, kamar yadda Babban Darakatan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kanon, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Lahadi
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!