Connect with us

MANYAN LABARAI

Harin tsana: Gwamnati Ta Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Guji Ramuwar-gayya

Published

on

Babban Lauyan gwamnatin tarayya, Alhaji Abubakar Malami, ya gargadi ‘yan Nijeriya da su guji kai farmaki ga harkokin kasuwancin kasar Afrika ta kudu da nufin yin ramuwar gayya a kan hare-haren nuna wariya da aka kaiwa ‘yan Nijeriya a can kasar.

Ranar Juma’a a Abuja ne Malami ya yi wannan maganar a lokacin da gamayyar kungiyoyin siyasa na, Integrity Political Parties (CIPP), suka ziyarce shi domin taya shi murna a kan sake nada shi Minista da aka yi.

Ministan ya koka musamman a kan kaiwa makeken kantin nan na Shoprite hari da wasu ‘yan Nijeriya suka yi domin mayar da martini a kan hare-haren nuna wariyar da aka kai, ya gargadi al’umma a kan daukan doka a hannun su.

“Wasu mutane ne da suke zaton kantin na Shoperite mallakin ‘yan kasar ta Afrika ta kudu ne, ba tare da sun san cewa kantin mallakin ‘yan Nijeriya ne ba.

“In ka je kantin shoperite z aka taras da baki-dayan ginin wajen ‘yan Nijeriya ne suke tafiyar da shi. Hakanan eiyoyin kamfanin sadarwa na MTN duk an baiwa wasu ‘yan Nijeriya kwangilar su ne.

“Don haka a she tattalin arzikinmu ne muke lalatawa, in harm un kulle wadannan kamfanonin tabbas milyoyin iyalai za su rasa ayyukan yi ka ga abin kanmu zai komo.

Ina da tabbacin babu wata gwamnatin da ta san abin da take yi za ta kyale ‘yan kasarta ko ‘yan kasar wajenta ana kasha su a kan titunan kasar ta.

Tun da farko, mai magana da yawun kungiyar, Dakta Yakubu Shendam, wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar, New Generation Party, ya yaba wa Malami ne a kan dagewar sa a wajen yakan cin hanci da karban rashawa a kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!