Connect with us

LABARAI

Masu Kyamar Baki Sun Yi Zanga-zanga Dauke Da Makamai A Afrika Ta Kudu

Published

on

Daruruwan gungun masu kyamar baki dauke da makamai sun gudanar da zanga-zangar neman baki ‘yan kasashen Afirka su yi gaggawar fice musu daga kasa, an yi wannan zanga-zangar ne yau Lahadi a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Masu zanga-zangar sun yi dafifi a wani dandali inda suke dakon Cif Butelezi Mangosuthu ya yi musu jawabi, Butelezi sannanen dan siyasa ne, kuma shugaban kabilar Zulu wacce tafi shahara a kasar Afirka ta Kudu.

A makon da ya gabata masu kyamar bakin sun aikata ayyukan ta’addanci akan baki, musamman in kasashen Nijeriya, Ruwanda, Malawi da Tanzaniya. Inda hare-haren nasu ya janyo ramuwar gayya a wasu kasashen ciki harda Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: