Connect with us

RAHOTANNI

Sharhi: Kuskure Ko Ganganci?

Published

on

A kwanan baya ne, hukumar fasa kwauri dake yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta kama wasu wukake da aka haramta da ake zargin kamfanin aikewa da sakwanni na FedEd ya shigo da su yankin na Hong Kong, kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike kan lamarin. An kuma bukaci FedEd ya gabatar da dukkanin abubuwan da ake bukata yayin bincike.

Wannan shi ne karo na biyu da kamfanin FedEd ya aikata irin wannan laifi, inda a watan Yunin da ya gabata ma, kamfanin ya shigo da wani kunshi dake dauke da bindiga cikin kasar Sin, matakin da ya keta doka da tsarin shari’ar kasar Sin.

A matsayinsa na kamfanin jigilar wasiku dake sahun gaba a Amurka, ya sha canja alakar kunshin kayayyakin da kamfanin Huawei ya ba shi da gangan, daga baya kuma ya ce kuskure ne.

Tun ba a je ko’ina, kamfanin ya sake aikata laifi, inda ya shigo da wasu haramtattun wukake cikin yankin Hongkong, matakin da ya bata suna da kimar kamfanin a fannin kasuwanci.

Amma ga kamfanin da ya shafe sama da shekaru ashirin yana harka a kasar Sin da sauran sassan duniya, dole ya san dokoki da ka’idojojin da suka shafi na’u’oin kayayyakin da kowace kasa ta yarda a shigo da su cikin kasarta, don haka, abin da kamfanin ya aika, kuskure ne ko ganganci? Sannan masu hulda da shi za su sake yarda da shi ko a’a? Zabi ya rage ga mai shiga rijiya.

Don haka, duk kamfanin jigilar kaya dake son cin gajiyar kasuwar jigilar kayayyaki mai kyakkyawar makoma a kasar Sin, dole ya mutunta doka da tsarin shari’ar kasar. Ko shakka babu, ba wasu kamfanonin ketare ko daidaikon mutane, da Sin za ta bari su rika keta doka da tsarin shari’arta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!