Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Bawan Mata’

Published

on

Suna: Bawan Mata

Tsara labari: Zaharaddeen A. Satatima. 

Kamfani: Dogon Yaro Mobie Tone.

Daukar Nauyi: Anas A.U Mafara.

Shiryawa: Abdullahi Dogo.

Bada Umarni: Babangida Bangis.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad

Jarumai: Rabi’u Daushe, Musa Mai Sana’a, Ado Gwanja, Rabi’u Rikadawa, Fati Shu’uma, Raha Iman, Ayatullahi Tage, Hauwa Yare, Ahmad Sultan, Malam Lawan da sauransu.

Fim din Bawan Mata fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani Dan Sanda (Rabi’u Daushe) Wanda ya kasance ba shi da wani abun yi sai yi wa mata hidindimu na kudi, Amma ko kadan ba ya iya samun kashewa mahaifiyarsa ko da nera daya. A kodayaushe idan ta tambaye shi kudi sai dai ya ce mata shi fa bashi da ko sisi. A fitowa ta farko a cikin fim din an nuno mahaifiyar tashi ta na fada masa ya ba ta kudi sai ya ke ce mata shi ba shi da komai sai nera goma, Amma ya na fitowa waje sai ga shi ya bawa yarinyarsa Zahra( Fati Shu’uma) dubu biyu domin ta je ta biya kudin hayar daki da a ke bin ta.

A dayan bangaren, shi ma (Rabi’u Rikadawa) a na shi bangaren haka ya ke hana matarshi kudin cefane amma kuma ya zo ya tafi gidan masu zaman kansu ya je ya kashe kudadensa.

A wani bangaren Kuma, (Ado Gwanja) shi ne mamallakin gidan da wadannan mata masu zaman kansu su ke zaune, Kuma shi ne mai kulla duk wata harkalla da a ke hadawa a wannan gida. A haka dai su ka ringa rayuwa su hana iyayensu da iyalensu komai a gida amma su fito su kashewa mata a waje.

Shi kuwa Ofisa ( Daushe) da barikin ta yi masa dadi, sai ya dage sai ya auri yarinyarsa ta barikin wato Zahra, Wanda kuma a karshe ya samu nasarar aurenta, inda shi wannan kawalin (Ado Gwanja) ya bayar da aurenta ga shi Ofisa, Kuma su ka sha shagalin bikinsu a dai cikin wannan gida nasu na barikinsu.

Duk da cewa mahaifiyar Ofisa ko kadan ba ta goyi bayan auren shi da Zahra ba, amma haka ya dage a kan sai ya aure ta, kuma karshe ya aure ta din. Sai dai tun kan a je ko’ina auren ya lalace bayan an tabbatarwa Ofisa cewa ya na dauke da cutar kanjamau wadda Zahra ta sanya masa kuma ta tsallake ta gudu ta bar gidan. Haka dai ta tafi ta bar shi cikin nadamar abubuwan da ya aikata da kuma zaman jiyar cutar da take damun shi.

Abubuwan Yabawa

1. Sunan fim din ya dace da labarin fim din.

2. Ana nuna tasirin da sabawa iyaye yake sa shi wajen samun mummunan sakamako ga duk wanda ya zamo mai saba mu su da kin yi mu su biyayya.

3. An nuna irin mummunan sakamako da biye-biyen mata kan iya haifarwa.

4. An samu sauti mai kyau a cikin fim din.

Kurakurai

1. Daukar hotuna ba ta yi kyau ba yadda ya kamata, domin kuwa hotunan sun yi dishi-dishi a gurare da yawa.

2. An samu wuce gona da iri a cikin fim din wato( Ober Acting).

3. Kalaman da Ofisa ya ke yi wa mahaifiyarsa, sam-sam ba su dace da irin kalaman da d’a ya ke yi wa mahaifiyarsa ba.

4. An samu amfani da wasu kalamai da yawa da bai kamata a ji su a cikin fim din ba.

Karkarewa

Fim din Bawan Mata, fim ne da ya samu nasarori da kuma akasin haka. Amma ya na da kyau a ringa tantance kalamai da yanayi, ta yadda yadda yadda za su ringa tafiya dai-dai tsarin na addini da kuma al’ada. Fatanmu a kodayaushe shi ne ganin an inganta harkar domin samun nasarori marasa adadi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!