Connect with us

NAZARI

Tarihin Sufeton ‘Yan Sanda Guda 11 Da Aka Yi A Nijeriya Cikin Shekara 20

Published

on

 Tun bayan da kasar nan ta koma mulkin dimokradiyya a shekarar 1999, bayan shudewar mulkin soji, rundunar ‘yan sandar Nijeriya ta samu shugabanni daban-daban. Ga tarihin guda 11 daga cikin su.

Musiliu Adeola Smith:

A farkon jamhuriya ta hudu a shekarar 199, aka nada Alhaji Musiliu Adeola Smith a matsayin shugaban rundunar ‘yan santa na kasa, wanda ya gaji Ibrahim Coomassiea lokacin mulkin soji a shekarar 1993.

A lokacin da ya ke gudanar da  aiki a rundunar ‘yan sanda, ya yi aiki a sassa daban-daban na kasar nan, inda ya fara aiki daga Inugu a matsayin mataimakin sufiritanda na ‘yan sanda a shekarar 1972. Daga baya ya zama jami’an gudanar wa a kwalejin ‘yan sanda da ke Ikeja, sannan ya kuma zama DPO ‘yan sanda a garin Mubi cikin Jihar Adamawa. A shekarar 1980 zuwa 1982 ya jagoranci ‘yan sanda na musamman a Alagbon, inda daga baya aka maida shi zuwa garin Ilorin domin gudanar da wasu ayyuka na daban. An dai nada shi a matsayin mataimakin shugaban ‘yan sanda a cikin shekarar 1996. Sannan an cire shi daga shugabancinsa bayan da ya shekara uku, kafin ya kare wa’adin mulkinsa na farko, wanda shugan kasa Obasanjo ya nada shi a watan Maris na shekarar 2002, sakamakon yajin aiki da rundunar ‘yan sanda ta gudanar.

Tafa Balogun

Bayan ya kammala jami’ar Jihar Legas, Balogun ya shiga cikin hukumar ‘yan sanda a watan Maris na shekarar 1973. Ya gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na cikin kasar nan, inda daga baya ya zama dogarin tsahon shugaban ‘yan sanda na kasa, Muhammed Gambo, daga nan ya zama mataimakin kwamishinan Jihar Edo, Ribas da kuma Abiya. Ya zama mataimakin shugaban ‘yan sanda mai kula das ashen Zone 1 da ke garin Kano. Tsohon shugaban ‘yan sandar na kasa ya tabbatar da tsare rayukan jama’a a kasar nan lokacin da ya ke jagorantar hukumar. Ya samar da kariya ga ‘yan sanda lokacin da ake gudanar da babban zabe a watan Afrilun shekarar 2003, domin kada a ci zarafin ‘yan sandan. A watan Agustan shekarar 2003, ya kaddamar da mujalla mai suna “Nigeriya: Electoral Biolen

National Security”, domin ilmantar da ‘yan kasa dokokin zabe, yadda ake gudanar da jam’iyu da kuma sanin kyakykywan gwamnati kamar yadda tsarin mulki ta tanada. A karshen shekarar 2003, ya kaddamar da tsaro a duk fadin kasar nan, domin kar a samu rikici lokacin da ake gudanar da taron kungiyar rainon Ingila.

A karshen shekarar 2004, aka fara zargin cewa, shugaban ‘yan sandar da cin hanci da amsar rashawa daga wurin ‘yan siyasa. An dai gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya da ke garin Abuja, a ranar 4 ga watan Afrilun shekarar 2005, bisa tuhumar sa da karkatar da kudi har naira miliyan 13. An dai gabatar wa kotun hujjoji a kan kaddaro da kuma kudade wanda ya mallaka ba bisa ka’ida ba. Kotu ta yanke masa zama a gidan yari na tsawan wata shida, inda aka sake shi bayan ya kammala zama a gidan yari a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2006.

Sunday Ehindero

Shi dai Sunday Gabriel Ehindero ya rike mukamin shugaban ‘yan sandan Nijeriya tun daga shekarar 2005 har zuwa 2007. Ya fara aiki ne a matsayin malamin makaranta a garin Abeokuta da ke cikin Jihar Ogun, inda ya shiga aikin dan sanda a karni na 70. Kafin ya zama shugaban ‘yan sandar Nijeriya, Ehindero ya jagoranci tawagar ‘yan sanda wadanda suka gudanar da bincike a kan masu yin tsafi da mutane a yankin Okija Shrine cikin Jihar Anambra, a watan Afrilun shekarar 2004.

Bayan ya zama shugaban ‘yan sandar Nijeriya, a nasa shugabancin ya samar da tsare-tsare daban-daban, inda har ya bukaci ‘yan majalisa su samar da kudiri a kan wariyar ga rundunar ‘yan sanda.

Lokacin da babban zabe ya gabato a shekarar 2007, Ehindero ya bayyana yadda ‘yan sanda za su dakile duk wata rikici da ta taso. Ya bayyana cewa, an bai wa ‘yan sanda bindigogi guda 80,000 da kuma harsasai guda miliyan 32 domin dakile duk wani aikin ta’addanci.

Bayan ya yi riyaya, an dai zargi Ehindero da damfarar naira miliyan 21, sannan karkatar da kudaden ‘yan sanda na naira miliyan 2.5 da kuma naira miliyan 300 wanda ake zargi ya karkatar da su wajen gina gidajen ‘yan sanda.

Mike Okiro           

Shi dai Mike Mbama Okiro ya rige mukamin shugaban ‘yan sanda tun daga shekarar 2007 har zuwa 2009. Okiro ya shiga aikin dan sanda ne tun a shekarar 1977, inda ya zama DPO a ofishin ‘yan sanda daban-daban a Jihar Legas, ya rike mukamai da dama a cikin aikinsa. Bayan a zama shugaban ‘yan sandar Nijeriya, farkon abin da Okiro ya maida hankali dai shi ne,  a samu cikakken tsaro a Nijeriya tare da kokarin shigar da Nijeriya cikin kasashe guda 20 masu karfin tattalin arziki a duniya kafin shekarar 2020. Ya kara bunkasa jin dadin ‘yan sandar Nijeriya wajen kara musu albashi da kuma samar da kayayyakin aiki ga ‘yan sanda.

Okiro ne ya kaddamar da rajistar ayin waya a cikin kasar nan, ya kaddamar da rundunar ‘yan sanda masu yaki da ta’addanci, sannan ya tausasa wa bankuna masu zaman kansu saka na’urar talabijin da mallakar motoci masu sunke da kuma samar da kofofi wanda harsashi baya huda su, domin rage fashi da makami a bankuna. Ya kuma masar da gasar ‘yan sanda a watan Oktoban shekarar 2008.

Ogbonna Onovo

A cikin watan Yulin shekarar 2009, Ogbonna Okeckukwu Onobo, ya zama shugaban ‘yan sanda na Nijeriya har zuwa watan Satumbar shekarar 2010. Shi ne shugaban ‘yan sanda na farko daga yankin kodu maso gabas. Ya dai kammala karatunsa ne a jami’ar Nijeriya ta Nsukka, sannan ya shiga aikin dan sanda a watan Agustan shekarar 1977, ya zama kwamishinan ‘yan sanda a watan Afrilun shekarar 1997. An dai fara tura shi aiki ne a Jihar Ribas, inda daga baya aka tura shi Imo, Legas, Edo, Adamawa da kuma Jihar Ogun. A tsakanin shekarar 1998 da 2000, shi ne shugaban hukumar sha da fataucin muyagun kwayoyi. Onobo ya zama mataimakin ‘yan sanda a ranar 14 ga watan 2002, ya dai yi aiki da tsofaffin shugaban ‘yan sanda guda uku wanda suka hada da Tafa Balogun, Sunday Ehindero da kuma Mike Okiro. Shi ne mukaddashin shugaban ‘yan sanda kafin a nada Mike Okiro.

Hafiz Ringim:

Hafiz Ringim ya yi alkawarin dakile ayyukan Boko Haram lokacin da ya gaji Onobo a shekarar 2010. Ringim yana cikin sufetoci guda 1,1977 wadanda aka tura sassa daban-daban, a watan Maris, domin kasar tana fuskantar tada kayar baya na ‘yan kungiyar Boko Haram. An dai samu firgici a lokacin da aka kai hari a shalkwatan ‘yan sanda da ke Abuja, a watan Yunin shekarar 2011, bayan kwanaki shida ya yi alkawarin dakile kungiyar lokacin da ya ziyarci Maiduguri, inda lamura suka kara kazanta. An dai samu tashin bama-bamai da dama a lokacin mulkinsa, wanda ya fi kamari dai shi ne, ranar Kirsimeti wanda ya faru a cocin St Theresa Catholic Church, a garin Madalla kusa da Abuja, inda aka yi asarar rayukan mutane guda 40,sannan an samu asarar rayuka a garin Kano wanda ya kai 185.  Ya yi ritaya a ranar 25 ga watan Junairun shekarar 2012.

Mohammed Dikko Abubakar:

An nada Mohammed Dikko Abubakar a matsayin shugaban ‘yan sandar Nijeriya a shekarar 2012. Abubakar yi aiki tukuru bayan ritayar Ringim a shekarar 2012. Kafin wannan lokaci dai, ya rike mukamin mataimakin shugaban ‘yan sanda mai kula Zone 12 da ke garin Bauchi. Ya kuma rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas. Abubakar ya bayyana cewa, duk wanda aka cafke da laifin cin hanci da rashawa da kuma rashin gudanar da aiki yadda ya kamata a cikin ‘yan sanda, to za a kore shi daga aiki, amma duk da haka ya kasa dakile lamarin. Ya yi ritaya a shekarar 2014.

Sulaiman Abba:

An dai nada Sulaiman Abba a matsayin shugaban ‘yan sanda na Nijeriya a watan Agusta na shekarar 2014, bayan da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi a matsayin mukaddashin shugaban ‘yan sanda. Inda daga baya ya tabbatar da shi a matsayin shugaban ‘yan sanda na Nijeriya a ranar 4 ga watan Nuwamba. Kafin wannan mukami dai, Abba rike kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas da kuma Jihar Ribas, sannan ya rike mukamin mataimakin shugaban ‘yan sanda mai kula da Zone 7 da ke Abuja. An dai sallame shi daga aiki a ranar 21 ga watan Afrilun shrkarar 2015, domin rashin da’a.

Solomon Arase:

Shugaban kasa Jonathan ya nada Solomon Ehigiato Arase a matsayin shugaban ‘yan sanda wanda zai maye gurbin Sulaiman Abba, a shekarar 2015. Kafin a nada shi a matsayin shugaban ‘yan sanda, Arase shi ne shugaban ‘yan sanda na sashen masu basira. Ya dai fara aikin dan sanda a shekarar 1981. Lokacin da ya ke aikin dan sanda, Arase ya rike mukamai da dama ciki har da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Akwa Ibom da kuma mataimakin shugaban sashe. Arase ya yi ritaya a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2016.

Ibrahim Kpotun Idris: 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Kpotun Idris a matsayin shugaban ‘yan sanda a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2016. Kafin wannan lokaci dai, Idris ya rike mukamin mataimakin shugaban ‘yan sanda na Abuja. Ya kuma jagoranci ‘yan sandan mobayal, sannan ya rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda a Kano da kuma Nasarawa a lokota daban-daban. Ya yi ritaya a ranar 15 ga watan Junairu.

Mohammed Abubakar:

Mohammed Abubakar dai shi ne ya ke rike da mukamin shugaban ‘yan sanda na Nijeriya a halin yanzu. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin shugaban kasa a ranar 15 ga watan Junairun shekarar 2019. Kafin ya zama shugaban ‘yan sanda, ya rike mukamin mataimakin shugaban ‘yan sanda na garin Benin da ke Jihar Edo. Adamu yana shirin daukar ‘yan sanda guda 10,000 a yanzu haka.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: