Connect with us

WASANNI

Ahmad Musa Ba Zai Buga Wasan Najeriya Da Ukraine Ba Saboda Ciwo

Published

on

Dan wasan Najeriya, Ahmad Musa, wanda ya ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudiyya wasa ya fita daga cikin sansanin Super Eagles sakamakon ciwon da ya ji kuma ba zai buga wasan da kasar nan za ta fafata da Ukraine ba a gobe.

Tun da farko dai dan wasan yaji ciwo ne a kungiyarsa dake kasar Saudiyya a wasan da suka buga na baya bayan nan sai dai a haka ya tafi sansanin na Super Eagles amma daga baya likitocin tawagar suka tabbatar da cewa ciwon da yake dauke dashi bazai barshi ya buga wasan ba.

Musa ya buga wasanni biyu ne kacal a wannan kakar sakamakon ciwon da yake fama dashi inda ya buga  a wasan da suka fafata da Dhamk suka samu nasara daci 2-0 sai kuma fafatawar da sukayi Alfateh inda ya buga minti 59.

Ahmad Musa, mai shekara 26 a duniya zai kasance dan wasa na biyar acikin ‘yan wasan da suka samu ciwo kuma bazasu fafata wasan da Ukraine ba bayan dan wasan baya Kenneth Omeruo da Tyronne Ebuehi da Henry Onyekuru da Wilfred Ndidi.

Sai dai a sakamakon ciwon da ‘yan wasan suka samu kociyan tawagar ta Super Eagles ya gayyaci matasan ‘yan wasa irinsu Dennis Bonebenture daga Clubb Brugge da  dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bordeaud Josh Maja da Anderson Esiti daga kungiyar PAOK da kuma Bryan Idowu daga Lokomotibe Moscow.

Sannan rashin tsohon dan wasan Kano Pillars din, Ahmad Musa dan wasan baya, William Troost-Ekong, shine zai jagoranci tawagar a matsayin kaftin domin fafatawa da Ukraine wadda tsohon dan wasan AC Milan Andriy Shebchenko yake koyarwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: