Connect with us

RAHOTANNI

ALGON Ta Sauke Shugabanta Na Kasa

Published

on

Kungiyar kananan hukumomi  ta kasa (ALGON), ta tsige shugabanta na kasa, Mista Kolade Alabi Dabid.

Kungiyar ta ce, zaben da aka yi wa shugaban nata, wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Bariga a Jihar Legas, ya saba wa tsarin mulkin kungiyar.

Kungiyar ta nada mataimakin shugabanta, wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Soba a Jihar Kaduna, Mahmud Muhammad Aliyu, yam aye makwafinsa.

A cikin shawarar da kungiyar ta zartas a karshen taron da ta yi a Abuja, ALGON ta ce, shugaban karamar hukumar da ta tsige sam bas hi ma a cikin jerin sunayen shugabannin kananan hukumomi 774 na kasar nan, wadanda suke a cikin tsarin mulkin kasar nan na 1999, wanda aka yiwa kwaskwarima, don haka ba ta yanda za a yi ya jagorance ta.

Wannan sanarwar ta sami sa hannun Sakataren yada labarai na kungiyar na kasa, Andrew Alu.

Sanarwar tana cewa, “Kamar yanda sashe na 5 (1a) na tsarin mulkin ALGON ya nuna, wanda ya cancanci zama shugaban kungiyar tilas ne ya kasance zababben daya daga cikin kananan hukumomi 774 na kasar nan.

“Karamar hukumar shugaban kuwa ba ta a cikin jerin kananan hukumomi 774 na kasar nan.

“A kan haka, taron yay i gamayya a kan zaban shugaban karamar hukumar Soba, Honorabul Mahmud Mohammed Aliyu, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyar ta kasa, a matsayin sabon zababben shugaba na kasa, tun daga ranar 6 ga watan Satumba, 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: