Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Da Ya Kone Gidan Mahaifinsa Kurmus A Akwa-Ibom

Published

on

Wani magidanci mai suna Mista Okon Samson Udofia, ya bukaci gwamnatin Jihar Akwa Ibom tare da daukacin al’umman jihar su taimaka masa, a kan kona masa gida kurmus da dansa ya yi. Shi dai Udofia dan asalin kauyen Ikot Nya da ke cikin karamar hukumar Nsit Ibom ne, ya bayyana cewa rashin gida babbar matsala ce a wannan rayuwa.

Da ya ke yi wa manema labarai karin bayani, Udofia ya bayyana cewa, dansa mai shekaru 20, wanda ya na zargin ya samu tabun hankali, ya kone gidansa kurmus a ranar Laraba da misalin karfe tara na dare lokacin da ya ke barci. Ya kara da cewa, dansa barazana ne ga shi kansa da kuma al’umma gaba daya. Ya ce, ya bukaci ‘yan sanda su kawo masa dauki, amma lamarin ya ci-tura.

“Yarona fitinanne ne, ya na fama da dan karamin tabun hankali, na bukaci ‘yan sanda su cafke shi domin in kai shi asibitin mahaukata, amma ‘yan sanda su na fada min cewa, su ba aikinsu ba ne kama mahaukata. “Yarona hatsabibi ne har ya na yi min baraza sai ya kashe ni da kuma wasu mutanen kauyen. Cikin dare ya banka wa gidana wuta lokacin ina barci da misalin karfe tara na dare.

“Wutar ta kone gidan kurmus tare da kayayyakina wanda kudinsu ya kai naira 500,000. Allah ne ya sa na tsallake rijiya da baya. Wannan ba shi ne karo na farko da ya taba aikata irin wannan mummunan aiki ba,” in ji Udofia.

Ya cigaba da cewa, ya na jan kunnen mazauna kauyen Ikot Nya a kan yaronsa, idan ba an cafke shi an kai shi asibitin mahaukata ba, to zai iya kashe wani a kowani lokaci. “Ina kira ga ‘yan sanda da kuma gwamnatin jihar da su taimaka a damke yarona, domin kai shi asibitin mahaukata, ko kuma ya janyo babbar fitina.”

Wani mazaunin wannan kauye mai suna Udeme Uyoatta, ya bayyana wa manema labarai cewa, a yanzu haka mazauna kauyen ba su da kwanciyar hankali, saboda wannan matashi. Ya kara da cewa, mazauna kauyen sun bukaci DPO na ‘yan sanda da ya cafke yaron, amma sai ya na cigaba da cewa ba aikinsu ba ne kama mahaukata.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin DPO na ‘yan sandar yankin, amma wayarsa ba ta shiga har zuwa lokacin da a ke hada wannan rahoto.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!