Connect with us

RAHOTANNI

Dalilin Kotun Zabe Na Fatali Da Karar Da Aka Kai Hon. Doguwa

Published

on

Kotun sauraron kararrakin zabe ta ‘yan majalisun Jiha da na tarayya da ke zama a kan titin Miller, Kano, ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP ta shigar inda take kalubalantar zaben shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa, mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Doguwa.

Kotun mai wakilai guda uku a karkashin jagorancin Mai shari’a Nayai Aganaba ta yi riko da cewa, mai shigar da karan ya gaza tabbatar da zargin da yake yi wanda ya shafi aikata magudi a wajen zaben, aringizon kuri’u, tayar da rikici da kwatan akwatun zabe wanda aka shigar da karan a kansa.

Kotun ta ce maganganun da aka shigar na kalubalantar zaben na Alhassan Doguwa, suna da nauyi sosai, wadanda suka zama wajibi a tabbatar da sub a tare da wata tantama ba, kotun ta bayyana cewa, wasu ma daga cikin zarge-zargen sun shafi aokata laifi ne kai tsaye.

A cewar kotun, masu shigar da karan sun gaza janyo hankalin kotun a kan ainihin adadin da suke zargi a kansa wanda ya shafi aringizon kuri’u a wasu rumfunan zaben, ta kara da cewa, zargin yin aringizon kuri’un ba a hado shi da rajistar masu kada kuri’a ba, don haka sai zargin ya zama na banza kawai.

Kotun ta ce  ba a kuma gabatar mata da wani shaida a gabanta wanda ya shaida da cewa an hana shi, ko an hana ta kada kuri’a ba, don haka sai kotun ta yi watsi da zargin korar masu kada kuri’a kamar yanda masu shigar da karan suka yi zargi.

Da kotun take yanke hukunci a kan zargin shelanta sakamkon zaben karya a maimakon sakamkon zaben na gaskiya, Mai shari’a Nayai cewa yay i, tun farko har karshen shari’ar masu shugar da karan sun gaza gabatar da wani kwafi na ainihin sakamon zaben na gaskiya kamar yanda suke zargi.

Tun da farko, kotun ta yi fatali da karan da Jam’iyyar ta PDP ta shigar a kan sukar zaben da aka yi wa AbdulMumuni Jubrin Kofa(APC), wanda ke wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, a majalisar tarayya ta kasa.

Kotun ta ce, Jam’iyyar ta PDP ta gaza tabbatar da anyi zaben ne ba bisa ka’ida ba, wanda a kansa ne ta nemi kotun da ta soke sakamakon zabe, ta kuma shelanta dan takaranta Aliyu Datti na Jam’iyyar ta PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shugaban kotun, Mai shari’a Nayai Aganaba, yay i riko da cewa, zaben da aka yi a Bebeji da Kiru an yi su ne kamar yanda dokar zabe ta tanada, daga nan sai kotun ta umurci jam’iyyar ta PDP da ta biya tarar naira 200,000.

Hakanan kotun ta umurci jam’iyyar ta PDP da ta biya wata tarar ta naira 300,000 ga jam’iyyar APC, kotun ta bayar da wannan umurnin ne a bisa dalilin cewa jam’iyyar ta PDP ta gaza tabbatar da zargin da take yin a kalubalantar zaben dan majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar mazabar Minjibir da Ungoggo, a majalisar tarayya ta kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: