Connect with us

WASANNI

Everton Ce Kungiyar Da Ta Dace Da Iwobi – Joseph Yobo

Published

on

Tsohon kaftin din Super Eagles ta Najeriya, Joseph Yobo, ya bayyana cewa kungiyar kwallon  kafa ta Eberton ce kungiyar data fi da cewa da dan wasa Aled Iwobi na Najeria saboda zaifi kokarin da ake bukata.

Iwobi yabar Arsenal inda ya koma Eberton akan kudi fam miliyan 40 hakan yasa yafi kowanne dan wasa tsada a cikin tawagar Super Eagles a yanzu kuma a wasan da suka lallasa kungiyar Wolbes ya zura kwallo daya a raga.

Yobo mai shekara 39  a duniya wanda kuma yayi ritaya a shekara ta 2014 ya buga wasanni sama da 250 a kungiyar kwallon kafa ta Eberton cikin shekaru tara da yayi a kungiyar kuma yana fatan Iwobi shima zai kafa nasa tarihin a kungiyar a matsayinsa na dan Najeriya.

“Eberton ce kungiyar da tafi da cewa Iwobi ya koma domin buga wasa domin anan zai samu damar buga wasanni akai akai kuma kociyan kungiyar ya yarda da salon buga wasansa hakanne yasa ya sayoshi domin su taimaki juna” in ji Yobo

Ya cigaba da cewa “Kociyan Eberton ya iya koyar da kwallo kuma yasan yadda zai mayar da karamin dan wasa ya zama babba kuma kowa yaga yadda Iwobi yafara canjawa tunda kawo yanzu ya zura kwallo biyu a kungiyar”

Kawo yanzu dai Iwobi yana cikin sansanin Super Eagles ta Najeriya domin buga wasan da kasar nan zata fafata da kasar Ukraine a birnin Dnipro kuma bayan ya koma Eberton zasu fafata wasa da kungiyar Bournemouth da kuma Sheffield United duk a jere

A karshe Yobo yayi fatan Iwobi zaibi sahun ‘yan wasan Najeriya da suka buga wasa a kungiyar ta Eberton da suka hada da Yakubu Ayegbeni da Bictor Anichebe da shi kansa Yobo kuma yana ganin idan har ya dage zai zama babban dan kwallo a Eberton da Najeriya
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: