Connect with us

KASUWANCI

Fatara Ta Sa Boko Haram Kwace Naira Miliyan 15 Daga Sojoji

Published

on

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace makuden mudade sama da naira biliyan 15 tare da kayayyakin abinci da na masarufi a hannun sojojin Nijeriya- a wani kwanton bauna, da safiyar Jumu’a. Lamarin da ya jawo ji wa soja guda daya a harin.

Ayarin sojojin wadanda na rundunar sojoji ta ‘Super Camp 3’ da ta Bataliya ta 231- a rundunar yanki ta biyu da ke karkashin Lafiya Dole, a lokacin da suke jigilar kayayyakin su daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe, zuwa garin Biu, na jihar Borno, yayin da suka fada komar Boko Haram, kan babbar hanyar Azare zuwa Kamuya, da kimanin karfe  9:00 na safiyar ranar- kamar yadda majiyar sojoji ta bayyana.

Musayar wutar wadda ta murtuke tsakanin bangarorin, ya jawo soja daya ya samu rauni tare da barnata makaman sojojin masu yawa- inda mayakan suka yi awon gaba da motar yaki ta Bataliyar soji ta 231.

Haka kuma, maharan sun kwace makuden mudade kimanin naira miliyan 15,492,000; kudin da a ke kyautata zaton mudaden alawus din sojoji ne, wadanda suka doahi 20,000.

Kwanton baunar maharan wanda ya samu daukin Bataliyar runduna ta 27 da ke Damaturu, wanda ta halaka dan kungiyar daya. Yayin da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ce kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kashe sojoji guda biyu.

Bugu da kari kuma, wata majiyar rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana wa jaridar PREMIUM TIMES kan cewa ta halaka mayakan kungiyar Boko Haram, tare da kafewa kan cewa soja daya ya ji rauni a wannan hari na ranar Jumu’a. 

A na ganin ana samun ci gaba da kai wadannan hare-haren Boko Haram ta dalilin karancin kasancewar sojoji a jihohin Borno da Yobe, ta dalilin canjin wurin aiki. Yayin da rundunar sojojin ta bayyana cewa ta dauki matakin ne a kokarin ta na aiwatar da sabbin dabarun yaki a wasu wurare masu matsala a wannan yaki na arewa maso gabas.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!