Connect with us

LABARAI

Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Ci Gaban NIS A Karkashin Babandede

Published

on

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Mohammed Inuwa ya yaba da ingancin sabon fasfon Nijeriya da Hukumar Kula da Shige ta kasa (NIS) ta gabatar mai kunshe da abubuwa na zamani da kuma kyakkyawan tsaro.
Gwamna Inuwa ya bayyana haka ne Sa’ilin da ya ziyarci shalkwatar hukumar da ke hanyar filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Shugaban Hukumar Shige da Ficen, Muhammad Babandede MFR ya tarbi Gwamnan da kansa ba sako ba.
A lokacin ziyarar, an dauki bayanan Gwamna Inuwa domin yi masa sabon fasfo mai aiki na tsawon shekara 10 mai kunshe da bayanan lambar katin shaidar dan kasa (NIN), kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta wajabta daidaita bayanan sabon fasfono da na katin shaidar su zama bai-daya. Sanarwar da Jami’in yada labarai na Hukumar NIS, Sunday James ya raba wa manema labarai a madadin shugaban na NIS, ta bayyana cewa a takaitaccen jawabin da ya yi, Gwamna Inuwa ya jinjina wa irin kyakkyawan tsarin da aka yi wa sabon fasfon da kuma kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen karfafa Hukumar NIS domin ganin ta iya sauke nauyin da ke wuyanta inda hakan ya sa ake gudanar da sauye-sauye masu ma’ana na ci gaba da ya gani a shalkwatar hukumar.

Gwamnan ya yi alkawarin tallafa wa Hukumar NIS wajen shimfida ayyukanta na ci gaba a Jihar Gombe da kuma tabbatar da jami’an hukumar suna jin dadin gudanar da ayyukansu a jihar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: