Connect with us

KASUWANCI

Kisan Mutane Uku: Shugaban Karamar Hukuma Ya Koka Kan Harbin Da Jami’an Kwastam Suka Yi

Published

on

Shugaban karamar Hukumar Badagry ta Yamma,a Jihar Legas, ya koka a kan harbin da jami’an hukumar kwastam suka yi wa wasu mutane uku a yankin na su, sannan ya yi kira ga hukumomin da suka dace da su hukunta jami’in hukumar da ya aikata wannan mummunan abin. 

Mutane ukun da aka harba su ne,Afeez Sanumi, Yinusa Olatunji da Michael Amore. 

Cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen mako, Joseph yana cewa, “Ina rokon da a kwantar da hankali a kan harbin da aka yi ma mutanan wannan yankin namu su uku.

“Na yi tir da harbin da jami’an kwastam suka yi wa mutane uku, ina kuma yin kira ga hukumomi da su hukunta wadanda suka aikata wannan haharbin.

“Zan kuma tabbatar da an dauki matakin da ya dace na ganin an hukunta wanda ya aikata wannan aikin,  a kan hakan ina rokon da a kwantar da hankalo a zauna lafiya.

“Ya zama waibi duk mu taimakawa gwamnati a wajen hana shigowa da kayayyakin da a ka haramta shigowa da su ta kan iyakokinmu.

shugaban ya tunatar a kan yanda matasa a yankin su ka yi zanga-zanga a kan yadda jami’an na Kwastam suke uzzura masu a yankin.

“Sun koka a kan yanda jami’a na kwastam suke shiga gidajensu, hatta dakunan dafa abincinsu ma su na shiga su kwashe shinkafar da suka taras a ciki

“Sai dai abin takaicin shi ne yanda wani jami’in kwastam mai suna, Imokhe A.S, ya harbi wasu dalibai biyu ‘yan makarantar Sakandare da kuma wani mutum guda ba kuma tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Joseph ya bayyana kadan daga cikin abin da a ka tattauna a wani taron shiga tsakani na hukumomin tsaro wanda aka yi a fadar Alapa na masarautar Egun Awori, ya yi nuni da cewa, kwanturolan hukumar ta kwastam da sauran jami’an hukumomin tsaro duk sun halarci zaman.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!