Connect with us

WASANNI

Kwafsawar Manchester United A Kasuwar Cinikayyar ‘Yan Wasa

Published

on

Daukar dan wasa Aledis Sanchez daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ya na daya daga cikin kura-kuran da Manchester United ta yi a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa tun bayan da tsohon kociyan kungiyar, Sir Aled Ferguson, ya yi ritaya daga koyar da kungiyar a shekara ta 2013.

Duk da cewa Sanchez ya tafi kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan a matsayin aro na tsawon shekara daya, amma har yanzu Manchester United din ce za ta dinga biyan kusan kashi 60 cikin dari na albashin dan wasan.

Wasu su na ganin kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer, yayi kuskure da yabar dan wasan yabar kungiyar ba tare da ya sayi wani wanda zai maye masa gurbinsa ba har aka rufe kasuwar ‘yan wasan ya yinda wasu kuma gani sukeyi abinda yayi dai-dai ne.

Wani rahoto daya fita a satin daya gabata ya bayyana cewa har yanzu Manchester United zata dinga biyan dan wasan albashi duk satin duniya kuma sannan acikin yarjejeniyar da Inter Milan da Manchester United suka kulla babu maganar Inter din zata biya kudinsa a karshen kakar wasa.

Wannan kuma yana daya daga cikin kuskure da kuma rashin iya ciniki ga shugaban gudanarwar kungiyar, Ed Woodward ya nuna saboda har yanzu dan wasa Sanchez yafi kowanne dan wasa daukar albashi a kasar Ingila duk da rashin kokarinsa.

Acikin wasanni 45 da Sanchez ya bugawa Manchester United kwallaye biyar kawai ya iya zurawa a raga yayinda dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Norwich City, Pukki wanda kungiyar ta dauka ba tare data biya kudi ba wato (Free Transfer) ya zura kwallaye biyar cikin mintina 263 kacal a gasar firimiyar bana.

Har ila yau tura dan wasa Sanchez aro zuwa wata kungiyar nan ma ya nuna rashin kwarewa da sanin makamar aiki a Manchester United saboda wasu suna ganin gwanda Solkjaer ya zauna da dan wasan a wannan kakar domin gyara shi ya zama irin Sanchez din da aka sani a baya.

Solkjaer dai ya rabu da manya manyan ‘yan wasa a kungiyar ba tare da ya maye gurbinsu ba wanda hakan yasa kawo yanzu kungiyar babu manyan ‘yan wasa da yawa sai dai matasan ‘yan wasa masu kananun shekaru.

Dan wasa Maroune Fellaini shine dan wasa na farko da Solkjaer ta fara sallama a kungiyar saboda yana ganin bashi da gudunmawar da zai bashi kuma wasa daya kawai ya buga a kungiyar kuma shine wasan farko da kociyan ya jagoranci kungiyar da kungiyar Cardiff City a watan Disambar shekarar data gabata.

Amma kuma masu koyarwa irinsu Dabid Moyes, wanda ya sayo Fellani, da dan kasar Holland, Luis Ban Gaal da kuma mai koyarwa Jose Mourinho duka sunyi amfani da Maroune Fellaini kuma yayi musu amfani yadda yakamata.

Fellaini ya zura kwallaye masu amfani a Manchester United a lokacin da suke bukatar cin kwallo sannan kuma shine idan kungiyar tana neman tsira a hannun wata kungiyar take sakowa domin amfani da girmansa da tsawonsa.

Kuma kawo yanzu yana can a kungiyarsa ta Shandong Luneng yana buga wasa yadda yakamata yana zura kwallo a raga amma kuma tun bayan tafiyarsa har yanzu Manchester United bata sayi wani wanda zai maye gurbinsa ba.

Shima dan wasa Ander Herrera yabar Manchester United a lokacin da kungiyar take bukatar manya kuma kwararrun ‘yan wasa inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta kasar Faransa kuma an bayyana cewa tun bayan tafiyar Sir Aled babu wani dan wasa da kungiyar tayi nasara wajen sayansa kamar Herrera.

Wanda ya maye gurbinsa shine Scott McTominay saboda matashin dan wasa ne wanda bashi da tsoro sannan kuma yana buga abinda yakamata sai dai kawai rashin kwarewa yana damunsa saboda har yanzu matashi ne.

Kawo yanzu dai tsakiyar Manchester United bata da karfi sosai sannan shima dan wasa Fred, wanda kungiyar ta sayi daga Shakhtar Donesk ta kasar Ukarine ya kasa burge kociyan duk da cewa sun kashe makudan kudade wajen sayan dan wasan tsakiyar dan kasar Brazil.

Wani abin tambayar anan shine ta yaya Manchester United zata amince dan wasa kamar Ander Herrera yabar kungiyar kuma ba tare da sayan wanda zai maye gurbinsa ba? Wannan yana daya daga cikin matsalolin da kungiyar take ciki musamman a bangaren rashin iya shugabanci da tafiyar da kungiyar yadda yakamata.

Rumelu Lukaku shine dan wasan gaba ma kungiyar wanda babu kamarsa duk da cewa magoya bayan kungiyar sun nuna cewa basu gamsu da salon yadda yake buga wasa na amma kuma duk da ahaka a kakar wasan data gabata yafi Rashford da Martial zura kwallaye a raga kuma yanzu sune zasu zama masu ciwa kungiyar kwallaye.

Manchester United ta biya fam miliyan 75 wajen sayan Lukaku daga kungiyar kwallon kafa ta Eberton kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan gaba a gasar firimiya saboda ya shiga sahun ‘yan wasan da suka zura kwallo 100 a firimiyar Ingila.

Bayan kungiyar kwallon kafa ta Eberton ta lallasa Manchester United daci 4-0 a filin wasa na Goodison Park kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa akwai ‘yan wasan da dole sai sun bar kungiyar idan har suna son gyara matsalolinsu.

Acikin ‘yan wasan da suka wanann wasan akwai Lukaku wanda tuni yabar kungiyar sai Nemanja Matic, dan wasan tsakiya amma yanzu ya koma buga wasa a benci sai Fred shima yana benci sai Sanchez ya tafi Inter Milan zaman aro sai kuma Chris Smalling wanda shima ya tafi AS Roma zaman aro na shekara daya amma har yanzu Phil Jones yana nan.

Sai dai za’a iya cewa yanzu akwai canje-canjen da aka samu a kungiyar kuma sunyi amfani saboda kungiyar ta kashe kudi wajen sayan dan wasa baya, Harry Maguire akan kudi fam miliyan 80 sai Aaron Wan-Bissaka da kungiyar ta biya fam miliyan 50 daga Crystal Palace sannan kuma har ila yau sun biya fam miliyan 15 sun dauki Daniel James dafa Swansea City dake kasar Wales.

Za’a iya cewa duka ‘yan wasan da Solkajer ya sayo a lokacinsa suna kokari yadda yakamata kuma kungiyar ta fara gyara matsalolinta sai dai akwai bukatar kuma a watan Janairu a sayo dan wasan gaba mai taumakawa Martial da Rashford.

Masana kwallon kafa a kasar Ingila dai sun tabbatar da cewa idan har Manchester United ta bawa Solkjaer cikakken lokaci da kudin sayan ‘yan wasa zai mayar da kungiyar matsayin da aka santa a baya amma kuma sai anyi masa hakuri.

Manchester United dai ta sayi manya manyan ‘yan wasa a baya kamarsu Angel Di Maria da Lukaku da Sanchez da Pogba da Fred da Matic da Martial amma kuma basu samu canjin da suke bukata ba hakan yasa Solkjaer yace zaiyi amfani da irin salon da Sir Aled Ferguson ya dauka wajen sayan ‘yan wasan da suke son bugawa kungiyar wasa ba saboda da kudi ba sai don saboda suna son saka rigar kungiyar kuma suna alfahari da ita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!