Connect with us

KASUWANCI

Lantarki: Katsina Ta Biya Naira Miliyan 597 Ga Tashar Ajiwa

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da kwangila ta kimanin fiye da naira miliyan dari biyar da tis’in da bakwai domin samarwa da kuma sanya wasu injina masu amfani da wutar lantarki a sabuwar tashar samar da ruwa da ake gina a Ajiwa.

Haka nan kuma, an bayar da wata kwangilar ta samarwa tare da sanya wasu famfuna da sauran kayayyaki a tsohuwar tashar samar da ruwa dake Ajiwa akan kudi fiye da naira miliyan tis’in da bakwai.

An bayar da kwangilolin ga kamfanin continental computer wadda ake sa ran kammala kwangilar a cikin watanni bakwai da rabi da kuma wata shidda da rabi.

Babban sakatare a ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta jiha Alhaji Ubale Abdulrahman ya sanya hannu a madadin kwamishina Alhaji Salisu Gambo Dandume a inda Alhaji Ishak Abdullahi a ka ba shi kwangilar.

Kwamishinan ya roki dan kwangikar ya gudanar da aiki kamar yadda ya ke a yarjejeniyar kwangilar.

Alhaji Salisu Gambo Dandume ya jaddada kudurin gwamnati mai ci yanzu na samar da ingantaccen ruwansha ga al’ummar jihar Katsina.

Shi ma da ya ke jawabi manajan continental computer Alhaji Ishak Abdullahi yayi alkawarin gudanar da aiki na gari.

Ya gode wa gwamnatin jihar Katsina game da bayar da kwangilar ga kamfanoni na cikin gida.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!