Connect with us

LABARAI

Masifu: An Gudanar Da Addu’o’i A Jihar Katsina

Published

on

An gudanar da addu’o’i na musamman a jihar Katsina dangane da masifu da bala’o’in da su ka addabi al’ummar jihar. 

Taron addu’o’in wanda akayi shi a karkashin jagorancin Alh. Sabo Musa babban mai baiwa gwamna shawara ta fuskar habbaka cigaban jihar Katsina kwararren dan siyasa a cikin yan siyasar jihar Katsina wanda kuma kane ne ga mashahurin Malamin nan kuma shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Waikamatussunnah Sheikh Yakubu Musa Hassan. 

Taron ya gudana ne da misalin karfe goma na safiyar ranar Alhamis 5 ga Satumba, 2019 a Masallachin Tayoyi, wanda a ka fi sani da Masallachin Dahiru Mangal da ke Kofar Kwaya a cikin birnin Katsina. 

Dukkanin jama’ar jihar Katsina maza da mata, manya da yara da kuma tsofaffi sunyi tururuwa a babban masallacin domin halartar wannan taro da kuma gudanar da addu’a don samun saukin wadannan masifu. 

Manyan mutane, manyan Malamai daga kowane bangare, manyan jami’an gwamnati, yan kasuwa duk daga ko ina cikin fadin jihar nan sun sami halartar wannan taro wanda ya gudana. 

Daga cikin jami’an gwamnati da suka halarci wannan taro sun hada da Mai Shari’ah Musa Danladi Abubakar wanda ya wakilci maigirma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Alh. Aminu Bello Masari, maigirma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina Alh. Tukur Ahmad Jikamshi, Kakakin majalisar dokoki ta jihar Katsina Hon. Alh. Tasi’u Musa Maigari, da Danmajalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina Alh. Albaba, Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina, wakilan tsohon mai shari’ah na jiha kuma Galadiman Hakimin Malumfashi Alh. Sadik Abdullahi Mahuta da sauran manya-manyan jami’an gwamnati. 

Daga cikin manyan malamai da suka halarci wannan taro sun hada da Sheikh Yakubu Musa Hassan Shugaban kungiyar JIBWIS na jihar Katsina wanda ya samu wakilcin Malam Surajo Kankia shugaban majalisar malamai na kungiyar JIBWIS ta Katsina, Malam Abbate limamin Masallacin juma’a na tayoyi, Malam Aminu Usman (Abu-Ammar), Malam Ishaka Nuhu Batagarawa shugaban Munazzamatul fityanil Islam ta kasa reshen Jihar Katsina, Sheikh Husamatu Abbas Gambarawa, Sheikh Mukhtar Usman Jibia, Shehi Malam Namadi, Khalifa Sheikh Munir Sheikh Jafaru, Babban limamin masallacin juma’a na Katsina Malam Barira Musa, Hajiya Bilkisu Muhammad Kai-Kai, Hajiya Dr. Talatu Nasir da sauran su. 

Haka zalika, akwai wakilai na masu Martaba Sarkin Katsina Alh. Dr. Abdulmumini Kabir Usman da kuma sarkin Daura Alh. Umar Faruk Umar. 

Taron ya samu halartar kungiyoyi irin su kungiyar sha’irai ta kasa reshen jihar Katsina, kungiyar direbobi ta kasa reshen jihar Katsina, kungiyar yan jarida ta kasa reshen jhar Katsina, kungiyar ‘yan kur’aniyyun ta jihar Katsina da sauran kungiyoyi. 

Kafin fara gudanar da majalisin Limamin masallacin na tayoyi Sheikh Malam Abbate shine ya bude taron da addu’a. Inda daga bisani a yayin gudanar da taron aka gabatar da karatun Al-kur’ani maigirma, tasbihohi, zikirori da istigfari inda bayan nan Malamai daban-daban suka gudanar da addu’o’i iri-iri daban.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: