Connect with us

MANYAN LABARAI

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Najeriya Sun Tsallaka Nijar Neman Mafita

Published

on

An gudanar da tsaron kasa da kasa, don neman mafita dangae da matsalar tsaro da ta addabi wasu jahohin Najeriya  da su ka hada da satar shanu da garkuwa da mutane da sauran mayan laifufuka a jihar Maradi da ke jamhuriyar Nijar.

Taron dai ya samu halarta wasu daga cikin gwamnonin Najeriya da jahohinsu ke fama da wannan matsala ta ’yan bindaga da masu garkuwa da mutane da su ka hada da gwamnan jihar Katsina da Zamfara da Sakwatao da kuma na Maradi a jamhuriyar Nijar.

Da ya ke jawabin a wajan bude taron, gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa an shirya wannan taron cikin tsanaki domin tattauna wasu matsaloli da jahohin Najeriya guda hudu suke fuskanta.

Ya kuma kara da cewa taron zai kasance wani alami na  sake kafa tarihi na haduwa da shuwagabanin tsaro daga wasu jahohi domin tattaunawa tare da gano hanyar warware wannan matsalar tsaro

Gwamna Masari ya ce gwamnoni guda hudu daga kasashe guda biyu sun amince su yi aiki tare domin a tabbatar da an kawo karshen satar shanu da aikata manyan laifufuka tare da tunkarar masu kawo cikas a yankin  jahohin sahel

Tunda farko a jawabin maraba gwaman jihar Maradi Alhaji Muhammad  Lawwali Issa  ya yi na’am da daukar nauyin wannan taro da ‘yan uwansa gwamnoni daga jahohin Katsina Da Zamfara da kuma sakwato suka shirya a Maradi ta jamhuriyar Nijar

Gwamnan na Maradi ya nuna kyakkyawar fata da cewa ya taba daukar nauyin shirya irin wannan taro kuma aka yi nasara saboda haka a wannan lokaci yana da fatan cewa za a tattauna abubuwan da za su kawo nasara.

Alhaji Lawwali Issa ya ce wannan taron tsaro da za a yi a jihar Maradi zai taimaka wajan gano hanyar da za a yi maganin wannan babar matsala da taki ci taki cinyewa a wasu jihohin arewacin Najeriya.

A nasa ta’alikin gwamnan jihar Sakwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi tunanin cewa wannan taron yana da alaka da cigaban sauran tarurukan tsaro da suka gudana inda ya ce, ana cikin laluben hanyar da za a magance wannan matsala ta rashin tsaro.

Daga nan sai ya yabawa shuwagabanin Najeriya da kuma na jamhuriyar Nijar wajan kokarinsu na ganin an dawo da zaman lafiya a kasashen guda biyu.

Haka kuma ya ce matsala tsaro abu ne da ya shafi kowa da kowa saboda haka sai ya ba  shuwagabanin tsaro daga jahohin hudun tabbacin bada duk wata gudinmawar da suke bukata domin yin wannan aiki mai tattare da kalubale

Sannan ya godewa gwamnan jihar Maradi saboda karamcin da ya nunawa ‘yan gudun Hijira daga jihar sakwato wadanda suka bar gidajansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Shima a nashi jawabin gwamnan jihar Zamfara Alhaji Muhammad Bello ya yi imanin cewa duk wani abu da zai samu wadannan jahohi daga karshe zai zame alheri da kuma cigaban su.

Ya kuma bayyana cewa matsalar satar shanu da garkuwa da mutane da sauran manya manyan laifufuka suna kara durkusan da harkokin yau da kullin a wadannan jahohi ya ce dole sai an hadu an yi maganinsu baki daya.

Ya kara da cewa tun lokacin shigarsa ofis mutane gama sha daya wadanda aka tabbatar ‘yan asalin Maradi da aka yi garkuwa da su a jihar Zamafara tuni aka hadu da ‘yan uwansu.

“Kafin a hadu su da ‘yan uwansu sai da aka dauke su zuwa asibitin jihar Zamfara domin duba lafiyarsu inda daga bisani aka bada umarnin maidu su jihar Maradi da ke jamhuriyar Nijar” in ji gwamnan.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: