Connect with us

LABARAI

Musulmi Sun Gudanar Da Bikin Hijira A Kogi

Published

on

A ranan Asabar da ta gabata ne, dubban al’ummar Muslmi su ka hallara a babban filin wasa da ke birnin lokoja inda su ka gudanar da bikin sabuwar shekara na addinin Muslunci, wato Hijira 1441.

 A jawabinsa na maraba a wajen bikin, shugaban majalisar malamai na jihar Kogi, wato Council Of Ulama’u wanda har ila yau shine babban limamin garin Ankpa, Sheikh Salman Adam ya shawarci al’ummar Muslmi dasu guji dukkan abubuwan da zasu gurgunta zaman lafiya a kasar nan.Ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin daukacin al’ummar jihar Kogi dama Nijeriya baki daya. Kazalika, sheikh Salman Adam ya kuma shawarci al’ummar Muslmi dasu gudanar da kawunansu kamar yadda suka kamata, musamman ma ganin cewa zaben gwamna da za a gudanar a jihar na kara karatowa, inda kuma yayi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin, lokaci da kuma bayan zaben.

Da ya ke gabatar da lakca, shugaban majalisar malamai na kasa, farfesa Muhammadu Alfakawi kira yayi ga Muslmi dasu ji tsohon Allah(SWT) tare da yin koyi da manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW)  Alkafawi yace  bikin yana nufin kauran da Annabi Muhammadu (SAW) yayi daga Makka zuwa Madina, sannan ya shawarci wadanda suke fuskantar matsaloli dabam dabam na rayuwa dasu yi imani da Allah wanda shike maganin komai.Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello wanda shine bako na musamman a wajen bikin, yayi kira ga al’ummar Muslmi dasu koyi darasa a bikin na Hijira a dai dai lokacin da yan Nijeriya ke kokarin gina kasar.

Gwamnan wanda kantomar riko na karamar hukumar Kotonkarfe, Barista Muhammed Tanko Osuku ya wakilta, yace Annabi Muhammadu (SAW) ya fuskanci tsananin wahalhalu da kuma kalubale dabam dabam daga Yan uwansa kuraishawa a birnin Makka, lamarin data tilasta masa da mabiyansa da suka yi imani da Allah yin kaura zuwa birnin Madina. Gwamna Bello ya kara da cewa sadaukarwa da hakuri da kuma juriya su suka taimaka wajen gina addinin Muslunci da al’umma bakidaya.A sabili da haka gwamnan ya bukaci al’ummar Muslmi dasu bada gudunmawarsu wajen ci gaban jihar Kogi,kana ya kara da cewa gwamnatinsa zata yi amfani da arzikin da Allah ya horewa jihar domin amfanin al’umma.

Shugaban bikin, Rt Hon Abdullahi Bello ya bukaci al’ummar Muslmi dasu ci gaba halaye abin koyi, sannan ya hore su dasu guji dukkan abubuwan da zasu gurgunta ci gaban kasar nan.Hon Bello har ila yau ya shawarci gwamnatoti a dukkan matakai dasu bullo da manufofi da kuma tsare tsaren da zasu rage zaman kashe wando da matasan kasar nan ke fama dashi ta hanyar samar musu da ayyukan yi. 

An karanto surorin kur:ani da maci wanda makarantun Islamiyya dabam dabam suka gudanar da kuma lancin kalandar sabuwar shekarar addinin Muslunci, kalandar Hijira.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: