Connect with us

LABARAI

NEMA Ta Hada Kai Don Kai Agajin Gaggawa Daura

Published

on

Hukumar NEMA ta kasa hadin gwiwa da takwararta ta jiha ta samar da kayan kayan jinkai ga wadanda ambaliyar ta ritsa da su a garin Daura. 

Kayayyakin na miliyoyin nairori sun hada da buhuna 300 na shinkafa dana wake dana masara da jarkunan man girki. 

Sauran kayayyakin sun hada da buhunan gishiri 50, gidan sauro 500 da buhunan siminti 1200 da buhunan kusa 8 da sili 750. 

A cikin sakon da ya aika dashi Gwamnan Jihar Katsina Alh. Aminu Bello Masari ya gargadi al’umma dasu guji zuba shara a kan hanyoyin ruwa domin kaucewa ambaliyar ruwan. 

Ya ce, gwamnatin jihar Katsina tana gudanar da aikin yashe hanyoyin ruwa a ciki da wajen birnin Katsina. 

Gwamnan wanda ya godewa Alh. Musa Hero akan nemo tallafin ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da abinda ya samu. 

Shugaban hukumar NEMA Engr. Mustapha yace tallafin zai baiwa wadanda abin ya shafa damar gyara gidajensu.

Tunda farko shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Daura Abba Mato ya godewa wadanda suka tallafamawa al’ummarsa. 

Idan za a iya tunawa wani mamakon ruwan sama kamar dab akin kwarya ta rushe gidaje daruruwa a garin Daura a makon da ya gabata. 

A cikin garin Katsina kusan dukkanin unguwannin da kaje zaka ga ruwan sama yayi barna inda ya tafi da dukiyoyin jama’a da dabbobi da makamantansu. Gwamnatin jihar Katsina da ‘yan kasuwa su na ta kai dauki ga mutanen da al’amarin ya shafa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: