Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ondo: Matashi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Hannun Matsafa

Published

on

Wani matashi wanda a ke zargin ya na da dan tabun hankali, ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu matsafa, a yankin Jubilee cikin garin Ikare Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta Jihar Ondo. Matashin wanda ba a ambaci sunansa ba, an tsince shi ne a kusa da makarantar Lennon Jubilee High School, bayan da su ka yi masa mummunan rauni da adda, inda su ka bar shi cikin jini. An bayyana cewa, matashin ya tsira ne lokacin da ya murgina zuwa wata bishiyar mangoro da ke kusa da makarantar St. Gregory Mega School, inda a ka tsince shi.

An bayyana cewa, ‘yan sanda daga yankin Ikare-Akoko su ne su ka tsinci matashi kwance cikin jini, inda su ka garzaya da shi zuwa asibiti, domin yin jinyar gaggawa, saboda a taimaki rayuwarsa.

An dai taba tsincen gawarwakin wasu mata guda biyu, a kan hanyar Ilepa a shekarar da ta gabata, matsafa sun cire musu gabansu kafin su ka yadda su a gefen hanya. Majiyarmu ta labarta mana cewa, ‘yan sanda su na fautar matsafan domin su damke su. Mafiya yawan masu shaguna a yankin Jubilee da kuma Idimango sun rufe shagonansu domin jin tsoron kar a kama su. 

Wakilinmu ya yi ta kokarin jin ta bakin DPO na ‘yan sandar yankin, Chika Odeh, amma lamarin ya ci-tura.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!