Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Ciki Da Magana’

Published

on

Suna: Ciki Da Magana

Tsara Labari: Ibrahim Y. Birniwa 

Kamfani: Family Inbestment

Shiryawa: Sani Mai Iyali

Umarni: Nazifi Asnanic 

Jarumai: Ali Nuhu, Maryam Yahya, Nuhu Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Hajiya Sadiya, Malam Haruna, Baba Labaran, Tsohon Lagos, Amina Muhammad Gombe. Da sauran su. 

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Abdulmajid (Ali Nuhu) yaje hira wajen budurwar sa inda yake tabbatar mata da cewar mutuwa ce kadai zata hana shi auren ta. Daga bisani kuma bayan dawowar sa gida sai mahaifin sa (Rabi’u Rikadawa) ya nuna wa Abdulmajid cewar akwai ‘yar yayan sa a kauye wadda zai aura masa, bai yarda Abdulmajid din ya auri wadda suke soyayya ba, hakan ne ya tashi hankalin Abdulmajid amma sai mahaifiyar sa ta kwantar masa da hankali ta hanyar nuna masa cewar idan yaje kauye yaga yarinyar matukar ta nuna bata son shi dole mahaifin sa ya janye maganar hada auren zumuncin.

Yayin da itama Halima (Maryam Yahya) tana da saurayin da suke soyayya dashi a cikin kauyen nasu, wanda har an saka musu ranar aure dashi, Saminu (Nuhu Abdullahi) shine yake tsananin son Halima domin a lokuta da yawa suna tare da juna shi da Halima suna hira. Kwatsam sai ga Abdulmajid yaje kauyen kuma ya sanar da Halima bukatar sa ta son auren ta, amma ya tabbatar mata da ba auren dole za’a musu ba idan bata son shi za’a janye maganar. 

Cikin mamaki kuwa sai Halima ta nuna ta amince da auren Abdulmajid duk da kasancewar an saka ranar auren ta da Saminu, ganin ta amince ne sai Abdulmajid ya nuna mata shi fa ba mutumin arziki bane, ya kasance mashayin giya, kuma manemin mata wanda har karuwa ya ajiye a gidan sa suke zaman dadiro. Jin hakan bai sa Halima ta canja ra’ayi ba, nan ta amince zata aure sa a hakan. 

Cikin lokaci kadan labari ya bazu a kauyen cewa Halima ta fasa auren Saminu dan uwanta Abdulmajid zata aura, hakan ne ya tashi hankalin Saminu domin Halima ta tabbatar masa da ta fasa auren sa ba kuma wai don bata son shi ba sai saboda wani dalilin na daban, sai dai kuma Saminu ya kasa fuskantar ta domin a ganin sa kudi ne yasa ta zabi auren Abdulmajid. Hakan ne yasa Saminu ya dauki matakin kuntata mata, ya zamana cewa ya raba Halima da kanwar sa wadda suke kawance, kuma ya fara goranta mata asalin ta yana nuna mata cewar abin kunyar da mahaifin ta yayi aka kore sa daga garin bai kai nata abin kunyar da ta aikata ba. 

Ita kuwa Halima bata biyewa Saminu sai dai takan nuna masa cewar da ace zai san dalilin da yasa bazata iya auren sa ba da haka rayuwar sa zata kare cikin kunci da zubda hawaye. Bayan dan wani lokaci aka yi auren Halima da Abdulmajid aka dauke ta daga kauye ta koma birni da zama can gidan Abdulmajid wanda mahaifin sa ya gina masa, sai dai tun a daren farko Abdulmajid ya sanar wa da Halima arziki dai zata ci sa amma bazata taba mallakar sa a matsayin mijin auren ta ba.

Tun daga wannan lokaci Abdulmajid ba ya ko shiga dakin Halima, haka ma idan tayi girki ba ya cin abincin ta, kafin wani lokaci ta fara laulayi da rashin lafiya, sai dai kuma Abdulmajid yana ganin halin da take ciki yaki kai ta asibiti, har sai da mahaifiyar sa tazo taga Halima a hakan ta sa aka kaita asibiti. Bisa mamaki kuwa sai aka gano cewar Halima tana dauke da juna biyu wanda kuma Abdulmajid ya tabbatar ba cikin sa bane, haka abin ya kai su har wajen mahaifin Abdulmajid (Rabi’u Rikadawa) wanda yaki bari a tattauna maganar dalilin hakan yasa suke zargin ko shine yayi mata cikin, hakan ne kuma yasa suka sake zaunar da Halima don jin wanda yayi mata ciki, a sannan ne ta tabbatar musu da cewar Mahaifin Saminu tsohon saurayin ta ne yayi mata ciki a wani lokaci da taje kai kudin adashi gidan sa yayi mata fyade. Fahimtar cewa tana da ciki ne yasa taki auren dan sa Saminu ta auri Abdulmajid don gujewa surutun kauye saboda mahaifin ta tsohon mazinaci ne me lalata da ‘ya’yan mutane kuma dalilin hakan ne yasa aka koreshi daga kauyen nasu. 

Jin hakan ne yasa Abdulmajid ya bukaci a yi karar mahaifin Saminu don shima a koresa daga kauyen kamar yadda aka kori mahaifin Halima daga cikin kauyen. Sai dai kuma Halima ta nuna rashin amincewar ta akan hakan domin kanwar Saminu kawarta ce bata son a tona musu asiri. Hakan ne yasa aka bar maganar. Bayan wani dan lokaci kuwa Abdulmajid suka hadu da Saminu a hanyar, a nan Abdulmajid ya sanar da Saminu abin kunyar da mahaifin sa yayi wanda shine dalilin da yasa Halima bata aure shi ba, sannan kuma yayi masa alkawarin bayan ta haihu zai saketa Saminu kuma ya auri masoyiyar sa. 

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa, sannan kuma labarin yayi nasarar rike me kallo, har zuwa ga sakon da ake son isarwa. 

2- Kalaman bakin jaruman sun yi dadi da ma’ana, wato “dialogue”. 

3- Daranktan yayi kokari sosai wajen ganin labarin ya tafi yadda ya dace ba tare da ya karye ba. Haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman ma sun yi kokari.

4- An samar da wuraren da suka dace da labarin.

5- Camera ta fita radau, sauti kuma sai dai ace ba laifi.

Kurakurai:

1- An samu “discontinuity” a lokacin da Abdulmajid (Ali Nuhu) yaje kauye gidan su Halima a karo na biyu, kofar gidan da ta fito ta tsaya suka yi hira, ba shi bane ainahin kofar gidan da aka nuna matsayin gidan su Halima.

2- Lokacin da mahaifin Atika ya kawo karar Malam Bala wajen Megari cewar Malam Bala ya yiwa ‘yar sa Atika ciki, abin daukar sauti ya fito wato “boom mic” a sa’ilin da wata budurwa a wajen take cewa Malam Bala ya taba bata kudi yace taje gonar sa ta sameshi.

3- Shin ina mahaifiyar su Saminu take ne? (Nuhu Abdullahi) har fim din ya kare ko sau daya ba’a nuna mahaifiyar su ba, duk da kasancewar akwai wuraren da ya dace a ganta, kamar lokacin da Saminu ya shigo don neman mahaifin sa bayan ya samu labarin cewar mahaifin nasa ne ya yi wa Halima ciki, da kuma wasu lokutan da ake nuna Saminu da kanwar sa a cikin gida su na tattauna matsalolin su, ya dace ko sau daya ne a nuno ta, saboda ba a nuna cewar ta mutu ba, domin me kallo yaga sanda Halima taje gidan da nufin kai mata kudin adashi.

4- Shin menene makomar soyayyar Abdulmajid (Ali Nuhu) da budurwar sa wadda yaso aure aka canza masa ita da Halima? Ya dace a karshen fim din ko a baki ne a fadi cewar zai koma gare ta, ko don tabbatar da maganar sa a farkon fim din ta cewar mutuwa ce kadai za ta raba su. 

Karkarewa: 

Fim din ya fadakar kuma ya nishadantar da me kallo, domin labarin ya isar da wani darasi musamman akan mazinata wanda suke bar wa ahlin su abin kunyar da ake goranta musu. Haka kuma an nuna karfin zumunci wanda al’umma zata iya yin koyi da hakan. Wallahu a’alamu! 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!