Connect with us

WASANNI

US OPEN: Andreescu Mai Shekara 19 Ta Doke Serena A Wasan Karshe

Published

on

Shahararriyar ‘yar wasan Tennis din nan, Serena Williams, wadda ta sake samun nasarar tsallaka wa zagayen karshe a gasar cin kofin US Open bayan da ta casa abokiyar wasanta, Elina Sbitolina, ta sha kashi a hannun matashiya Andreescu a ranar Asabar.

Serena Williams ta lashe gasar Grand Slam har sau 24 a wasan tennis, amma kuma ‘yar wasan mai shekara 37 ta samu koma-bya, inda ta sha kashi a hannun Andreescu da ci 6-3 7-5 a wani wasa mai zafi da su ka fafata a birnin New York na kasar Amurka.

Serena Williams, wadda ita ce ta takwas a duniya, ta yi kokarin samun nasara a gasa mafi girma ta Grand Slam karon farko, tun bayan da ta tafi hutun haihuwa a shekarar 2017, duk da cewa, gwarzuwar ‘yar wasan wadda ta taba lashe gasar har sau biyar a baya ta yi alkawarin doke Andreescu mai shekara 19 a duniya.

Andreescu dai ta casa abokiyar karawarta Belinda Bencic da ci 7-6 (7-3) 7-5, wanda hakan ya ba ta damar tsallaka wa zagayen karshen, sannan wannan ne karon farko da ‘yar wasan ’yar asalin kasar Switzerland ta shiga gasar US Open.

Mutane da dama su na ganin kamar Andreescu ba za ta iya doke Williams ba, saboda kwarewarsu ba daya ba ce kuma wannan ne karo na farko da za ta fafata da wata babbar ‘yar wasa kamar Williams a wasan karshe.

An haife ta ne bayan wata tara da samun nasarar farko da Serena Williams ta yi a gasar Flushing Meadows a 1999, sai dai da yawa su na ganin Williams a matsayin mace mafi kwazo a fagen Tennis, amma duk da haka alamu na nuni da cewa ‘yar wasan har yanzu ba ta gamsu da nasarorin da ta ke samu ba.

Williams ta doke ‘yar kasar Australia Margaret Court da yawan nasarori a gasar Grand Slam na ‘yan wasan dai-dai, amma kuma biyo bayan wahalar nakudar haihuwarta ta farko da har ta kusa rasa ranta, Serena ta samu nasarar kai wa zagayen karshe na gasar Wimbledon sau biyu a jere. Haka zalika a shekarar da ta gabata ne a ka samu rashin fahimtar juna yayin fafatawarta da Naomi Osaka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!