Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Wani Mutum Ya Gurfana Gaban Kotu Bisa Satar Naira 157,700

Published

on

Wani mutum mai suna Desmond Oboke Onobaibirhi dan shekara 28 da haihuwa, ya gurfana a gaban kotun Jihar Edo wacce ta ke da zama a yankin Oredo, bisa tuhumar sa da satar tsabar kudi har na naira 157,700. Ana dai zargin cewa, Desmond ya hada kai da wata mata mai suna Elisabeth Augustine, inda ya sace kudin daga bankin New Generation Bank, a ranar 12 ga watan Junairun shekarar 2019.

Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara ASP Patrick Agbonifo, ya bayyana wa kotu cewa, kudin mallakar wata mata ce mai suna Lobeth Tijani. Ana dai tuhumar sa ne da laifuka guda biyu wadanda su ka hada da na sata da kuma hada kai domin aikata laifi. Sai dai ya musanta laifin da a ke tuhumar sa da shi.

Lauya ASP Agbonifo ya bayyana cewa, wannan laifi ne wanda ya ke da hukunci a sashe na 390 da 516 na dokar manyan laifuka ta Jihar Edo wacce a ka yi wa garan bawul. 

Alkali mai shari’a Misis Ibie Akhere, ta bayar da belin wanda a ke tuhuma a kan kudi na naira 50,000 tare da mutum daya mai tsaya masa. Sannan ta dage sauraron wannan kara har sai zuwa ranar 9 ga watan Satumbar shekarar 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: