Connect with us

LABARAI

Adadin ‘Yan Nijeriya Masu Son Dawowa Gida Daga Afirka Ta Kudu Na Karuwa

Published

on

Mataimakiyar Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana wa manema labarai cewa akwai masu son dawowa Nijeriya da adadin su ya kai 649 daga Afrika ta Kudu.

Ta yi wa Kwamitin Majalisr Dattawa wannan bayani ne a lokacin da ta amsa gayyatar jin bahasi daga kwamitin kula da mazauna kasashen waje, a jiya Litinin. Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki kadan bayan da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya yi irin wannan ganawa da wannan kwamiti.

Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya tura jakada na Musamman, Ahmad Abubakar zuwa Afrika ta Kudun, domin ganawa da Shugaba Cyril Ramophosa. Tuni dai Abubakar ya dawo, kuma ya shaida wa Buhari abin da ganawar da ya je da shugaban Afrika ta Kudu ta kunsa.

Shi ma Shugaba Buhari ya bada odar gaggauta dawo da duk wani mai son dawowa gida Nijeriya. Kamfanin jirgin sama na Peace Air, ya sha alwashin dawo da masu son dawowa, duk da dai an samu tsaiko saboda rashin ingantattun takardun fasfo na wasu maso son dawowar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: