Connect with us

LABARAI

Dalilan Da Ya Sa ‘Yan Nijeriya Ke Shan Wahala- Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana dalilan da ya sanya ‘yan Nijeriya suke shan wuya. Inda shugaban kasar ya bayyana rashawa a matsayin daya daga cikin manyan abin da ke sanya miliyoyin ‘yan Nijeriya ke shan wuya a kasarnan.

Buhari ya kara da cewa; rashawa a kowanne mataki babban kalubalen ne da yake durkusar da tattalin arzikin Nijeriya tare da kawo cikas ga ci gaban kasar. Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara kan tattalin kudi da Makarantar koyar da tattalin kudi wato ICAN ta gudanar a Abuja.

Shugaban kasar wanda Sakataren gwamnati, Boss Mustapha ya wakilce shi, ya tabbatar da cewa yakin da suke yi domin kawo karshen rashawa a Nijeriya, na gaske ne, kuma nasarar wannan yakin ne kawai zai kawo ci gaba a gaba. Ya kara da rashawa rashawa kamar take hakki ne.

Sannan ya kara da cewa; rashawa yana durkusar da tattalin arziki, da rashin shugabanci nagari, da watanda da kudin al’umma da kuma durkusar da hannayen jari. Ya ce dole ne gwamnatinsu ta yaki rashawa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: