Connect with us

LABARAI

FOMWAN Ta Horas Da Mutum 50 Sana’o’i A Abuja

Published

on

Kungiyar mata Musulmi ta Nijeriya ta FOMWAN a birnin tarayya Abuja ta horas da mutum 50 sana’ar koyon dinki, girkin kayan makulashe domin ganin sun rike sana’o’in da za su dogara da kawukansu.

Horaswan ya gudana ne a karkashin kulawar FOMWAN da kuma NDE. Bayanai sun tabbatar da cewa; bayan sun kammala, an raba wa wadanda suka amfana da horon shaidar kammalawa wato satifiket a yayin taron kammala horaswan da ya gudana a ranar Talata a cibiyar FOMWAN din dake Abuja.

Malama Bola Usman, Amirar kungiyar reshen Abuja ta ce mutum 50 din an zabo su ne daga yakuna shida a wani mataki na kungiyar wajen bunkasa wannan wajen magance rashin ayyukan yi a tsakanin matasa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: