Connect with us

LABARAI

Nuna Kulawa Na Kange Mutum Daga Halaka Kansa- Shugaban Majalisar Legas

Published

on

Mudashiru Obasa, shugaban majalisar jihar Legas, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su rika nuna wa masu son halaka kansu soyayya da kauna, wanda ya ce hakan ne kawai zai sanya a rage yawan masu halaka kan su a Nijeriya.

Obasa, wanda ya kasance shi ne shugaban da ya jagoranci taron shugabannin majalisa, ya bayyana hakan ne a sakon da ya aika a ranar tunawa da matakan hana halaka kai.

Ya koka bisa yadda halaka kai wanda a da ba a san shi a Nijeriya ba, amma yanzu ya zama ruwan dare a kasar, wanda ya ce hakan ya faru ne sakamakon wadansu tasirin wasu abu wanda za a iya magance su. Shugaban majalisar ya nuna damuwarsa bisa yadda mutane ke dauke rayuwarsu akan abin da ya ce za a iya magance shi domin cimma nasarar rayuwarsu.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!